Connect with us

RIGAR 'YANCI

Sabon Alkalin Alkalan Kano Zai Sauya Fasalin Shari’a A Zamanance – Abubakar Khalil

Published

on

Tun a lokacin da mai girma Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada Dakta Tijjani Yusuf Yakasai, a matsayin Babban Alkalin Alkalai a Ma’aikatar Shari’a, ya zo da sabon tunani na sabunta wannan Ma’aikata ta shari’a a Kano, ta hanyar bijiro da wasu muhimman al’amura wadanda za su bunkasa Ma’aikatar ta yi daidai da ta zamani.

Mukaddashin Babban Magatakarda na Ma’aikatar ta shari’a na Jihar Kano,  Malam Abubakar Haruna Khalil ne ya bayyana haka ga mane ma labarai a ranar Juma’ar da ta gabata a Ofishinsa da ke Kano, inda ya fara da cewa a wannan zamani ne a karo na farko a ka maida dukkanin bayanai cikin kwamfiyuta baya ga wannan kuma aka maida shi internet wato yanar gizo-gizo kasancewar kowa ya san ma’aikatar shari’a ba ta wasa da tattara bayanai hakan ne yasaa yanzu duk wani bayani ya tashi daga cikin litattafai an sa shi kuma a internet domin ya kasance ba gar aba zago a dukkanin bayanan da ma’aikatar shari’a ta rubuta yana nan a ada ne.

Har ila yau, Khalil ya tabbatar da cewa, wani abu da kusan kowa ke yin farin ciki da shi a tsakanin Ma’aikatan shari’a da masu kawo kara ko korafi, don a tabbatar mu su da hakkinsu da suke nema a Kotuna shi ne, kirkiro da wani sabon sashi na sulhunta jama’a, wanda a ke kira ‘Alternatibe Dispute Resolution’ (ADR), yana matukar taka muhimmiyar rawa wajen warware matsaloli a tsakanin al’umma da kuma rage cunkoso a gidajen gyaran hali a yanzu, wanda kuma wannan sashi na sulhunta jama’a shi ne wanda a halin yanzu duniya take yayi, domin yanzu kuwa za a ga cewa akwai hanyoyi da dama da kasashen duniya da gwamnatocin duniya suka kirkira domin sasanta korafi ko kara a wajen Kotuna. Kazalika, idan wasu su ka hallara a gaban Kotuna, akan samu rashin jituwa a tsakaninsu, don haka ne Babban Alkalin Alkalai na Jihar Kano, ya tashi tsaye wajen kirkirar wannan sabon sashi a Ma’aikatar domin sulhunta jama’a, wanda kuma ya samu karbuwa ga jama’a, domin kuwa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu sakamakon samar da wannn sabon sashin karkashin jagorancin Alkalin Alkalan na Jihar Kano.

Baya ga wannan, an kuma sabunta hanyar da ake biyan kudin sallamar Ma’aikatan shari’a, wadanda suka kwanta dama ta hanyar zamani ta yadda kowanne Magaji akan sanya ma sa kudinsa a asusun ajiyarsa, idan kuma ba shi da asusu; wannan Ma’aikata ta umarci dukkanin wani mai hakki ko gado ya bude asusu domin a sanya masa kudinsa, don tabbatar da gaskiya da adalci da kuma mika hakki ga mai shi. Wannan sabon tsari shi ma a zamanin wannan Babban Alkalin Alkalai na Jihar Kano, Dakta Tijjani Yusuf Yakasai aka samar da shi a cewar ta Mukaddashin Babban Magatakarda na Ma’aikatar ta shari’a.

Haka nan, wani abin sha’awa da aka sake samu a wannan Ma’aikata ta shari’a shi ne, a wannan lokaci kaf shi ne mutum na farko da ya fara kirkirar Makarantar horar da Alkalai da sauran Ma’aikata, ta yadda za su samu ilimi mai zurfi da kuma gogewa, domin fuskantar kowane irin kalubale na tabbatar da sahihiyar shari’a mai cike da adalci da sanin ya kamata, wanda yanzu haka daf ake da yaye dalibai kimanin 26 ko ma sama da haka. Sannan kuma, wannan makaranta an yi ta ne domin Ma’aikatan Ma’aikatar shari’a da kuma masu sha’awar zama Alkalai na hakika kuma ana daukar kowanne dalibi ne gwargwadon matsayinsa da kokarinsa a kuma sanya shi a matsayin da ya dace, wanda yanzu haka wannan makaranta na kokarin samun amincewa daga Hukumomin da ke kula da bangare.

Har wa yau kuma, wani abu da ya zama abun alfahari shi ne samar da sassa ko sashi-sashi a wannan Ma’aikata ta shari’a har guda bakwai,  wanda wannan ya dada sabunta Ma’aikatar shari’a ta yi daidai da zamani, wanda yanzu haka akwai sashin ADR da mulki, sashin kudi da dai sauran sassa wanda hakan ya kawo cigaban wannan aiki, wanda duk abinda kake nema kasan inda za ka je ka same shi ba tare da bata lokaci ba, babu shakka wannan babban cigaba ne a wannan Ma’aikata ta shari’a da ke Jihar Kano.

A karshe Khalil ya bayyana cewa, duk wata nasara da aka samu an same ta ne sakamakon tsayawa tsayin daka da wannan Babban Alkalin Alkalai, Dakta Tijjani Yusuf Yakasai ya yi tare da nasarar da yake samu da goyon baya da kuma hadin kan Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Don haka, Ma’aikatar shari’a a shirye take wajen yin aiki ba tare da gajiyawa ba, duk da cewa duk wani cigaba baya rasa kalubale, musamman ga wasu mutanen da sai a hankali suke fahimtar wasu al’amura na cigaba, amma dai yanzu Ma’aikatar shari’a ta samu gagarumin cigaba a wannan lokaci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: