Connect with us

LABARAI

Kakakin Majalisar Dokokin Imo Ya Koma APC

Published

on

Shugaban majalisar dokokin jihar Imo Collins Chiji ya sauya sheka tare da wasu takwarorinsa bakwai sun fice daga jam’iyyar PDP sun koma APC mai mulki a jihar.

Collin Chiji ya sanar da sauya sanar da sauya shekarsu ne a lokacin zaman majalisar na yau Talata.

Sauya shekar ta ba wa jam’iyyar APC mai mambobi 18 rinjaye da kashi biyu bisa ukun ‘yan majalisar yayin da mambobi takwas.

Majalisar ta dage zamanta jim kadan bayan an sanar da sunayen ‘yan majalisar da suka sauya shekan, a cewar wasu jaridun kasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: