Connect with us

LABARAI

Mai Unguwa Ya Yi Kira Ga Matasa Su Nemi Ilimi Da Sana’a

Published

on

An yi kira ga matasan jihar Kano da na kasa baki daya cewa ya zama wajibi su ta shi tsaye wajen neman ilimin zamani da na addini, domin sai da ilimi rayuwa take inganta tare kuma da sana’oin da za su dogara da shi.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin mai unguwar Kwanar Jaba dake Gama dake cikin karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, Alhaji Mustapha mai unguwa alokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin shi dake unguwar ta Kwanar Jaba.
Mustapha mai unguwa ya kara da cewa duk al’ummar da suka cigaba sun same shi ne ta hanyar ilimi musamman idan suna aikin da ilimin da suka koya.Yawancin abin dake faruwa na rashin zaman lafiya a kasar nan da ma sauran wasu kasashen duk rashin ilimi ke haifar da su, saboda haka ya zam wajibi mu al’ummar kasar nan musan wannan musamman al’ummar da suka ito daga arewacin kasar nan.
Alhaji Mustapha ya nuna damuwar shi game da yadda a halin yanzu tarbiyar al’umma ta yi matukar karanci musamman ga matasa, idan ka kwatanta da shekarun baya, idan babba ya yi magana ana sauraran shi amma yanzu abin ya canja. Sannan wani kuma shi ne yawancin matasan mu ba su da tarbiya, wani abu kuma shi da yawa daga cikin su sun rungumi al’adun turawan yamma wannan na matukar barazana ga rayuwar mu musamman al’ummar musulmi maza da mata.
Mai unguwa ya yi kira ga iyayen yara cewa su kar matsa kaimi wajen kula da tarbiyar yaran da Allah ya ba su, su sani cewa Allah zai tanbaye su ranar gobe kiyama, har ila yau iyayen su san wadansu yara suke hulda da yaran su, su kuma tabbatar da cewa yaran na su suna da ladabi da biyayyada kuma girmama na gaba . Ilimi zai inganta ne idan aka ce dalibi yana da ladabi da biyayya, da kuma yi ma su addu’ar fatan shiriya .
Mustapha Mai unguwa ya yi anfani da wannan dama da kira ga gwamnatin jihar Kano a karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje , da ta samarwa da unguwar ta kwanar Jaba da makarantun sakandare ta mata domin yanzu haka babu sakandare ta mata , sai sun shiga cikin unguwar sabongari wanda wannan na matukar barazana ga tarbiyar su musamman ta addini da kuma al’ada.
Wani abu kuma da yankin yake bukata shi ne Ruwa da kuma hanyoyi, hanyoyin da ake da su yanzu sun matukar lalacewa, sabodahaka yana da kyau gwamnatin ta Ganduje ta waiwayi wannan yankin , saboda al’ummar yankin na matukar biyayya ga gwamnatin ta Ganduje.
Daga karshe mai unguwa Mustapha, ya yi addu’ar Allah ya baiwa jihar Kano da kasa bakidaya zaman lafiya da karuwar arziki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: