Connect with us

LABARAI

Matsalar Tsaro: Dan Majalisar Dattawa Ya Bukaci Buhari Ya Yi Murabus

Published

on

Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon rashin tsaron da ya adddabi kasar a baya-bayan nan.

Sanatan yana wannan magana ne a zauren majalisar ranar Laraba yayin da ‘yan majalisar ke tafka muhawara kan wani kudirin tsaro da Sanata Yahaya Abdullahi ya gabatar tare da goyon bayan sanatoci 105.

‘Muhimmin aikin da ya kamata a yi a Nijeriya ba a yi shi ba. Muna neman wannan gwamnati ta yi murabus saboda babu abin da za ta iya yi a kasar nan.’ in ji Sanata Abaribe.

Kudirin na Sanata Yahaya Abdullahi, wanda ya samu goyon bayan sanatoci 105, ya bukaci gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta-baci kan harkar tsaro a kasa baki daya sannan kuma a kafa wani kwamiti na musamman da zai yi aiki da jami’an tsaro sannan ya bayar da rahotonsa ga Majalisar Dattijai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: