Connect with us

WASANNI

An Kai Wa Gidan Shugaban Gudanarwar Manchester Hari

Published

on

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa wasu wadanda ba a san ko su waye ba sun kai hari a gidan shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ed Woodward, a ranar Talata da daddare.

Sakamakon rashin kokarin kungiyar a cikin filin wasa da kuma rashin sayan sababbin ‘yan wasa yasa magoya bayan kungiyar suka rera waka acikin fili a lokacin da kungiyar take buga wasa da kungiyar Burnley a satin daya gabata.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar wasu matasa da yawansu ya kai mutum 20 ne su ka kai wa gidan shugaban hari inda suka dinga jefa wuta a gidan domin kona gidan kafin a ankarar da jami’an tsaro.

Tuni kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta mayar da martani bisa abinda yafaru inda tayi Allah wadai da halayyar da wasu daga cikin magoya bayan kungiyar suka nuna kuma ta tabbatar da yin bincike domin hukunta wadanda aka kama.

“Mun san cewa duniya zata goya mana baya a kokarin da mukeyi tare da ‘yan sandan birnin Manchester domin gano wadanda suka aikata wannan aiki domin mu gurfanar dasu a gaban kotu a hukuntasu” in Manchester United

Kungiyar ta kara da cewa “Duk wanda aka kama yana da hannu a wannan mmuunan laifin da aka aikata zai fuskanci fushin kungiyar domin zata hanashi kallon wasan kungiyar har abada sannan kuma zai fuskanci fushin hukuma”

Sai dai har yanzu babu tabbacin ko Woodward da iyalansa suna gidan lokacin da abin yafaru amma kuma jami’an tsaro sun tabbatar da faruwan abin kuma tuni suka shiga bincike domin gano wadanda suka aikata
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: