Connect with us

LABARAI

Gwamna Zulum Ya Nada Ibo Da Bayarabe Mukami

Published

on

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Laraba ya kaddamar da masu ba shi shawara 26 domin ganin sun taimaka masa wajen gudanar da harkokin jihar.

Daga cikin masu ba shi shawarar harda Inyamuri daga karamar hukumar Dunukofia ta jihar Anambra, Kesta Ogualili da kuma Bayerrabe mai suna Yusuf Alao, daga karamar hukumar Ogbomosho ta jihar Oyo.

Kakakin Gwamnan, Isa Gusau, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a garin Maiduguri a ranar Laraba.

Gusau ya ce mataimakin gwamnan, Umar Kadafur, shi ne ya jagoranci zaman rantsawar a ranar Laraba gidan gwamnati dake Maiduguri.

Ya kara da cewa gwamnan a ranar 9 ga watan Janairu ne ya amince da nadin mutum 26 a matsayin masu taimaka masa a sha’anin mulkin jihar, ciki kuwa harda mutum biyu wadanda ba ‘yan asalin jihar bane. Amma an ba su mukamin ne bisa yadda suka bai wa jam’iyyar APC goyon baya a jihar.

Daga cikin wadanda aka nada sun hada da; Sheikh Modu Mustapha, Ali Damasak, Mustapha Bulu, Hussaini Gambo, Bukar Ardoram, Tukur Mshelia, da Tijjani Goni.

Sai kuma Mustapha Sandabe, Gadau Ngurno, Mohammed Maulud, Bole Kachallah, Abdulrahman Abdulkarim, Bashir Maidugu, Bukar Konduga, Umoru Gaya da Ali Zangeri.

Sauran sun hada da; Tukur Ibrahim, Tijjani Kukawa, Abba Gubio, Gana Badu, Adamu Chibok da Ahmed Asheikh-Zarma.

Sai kuma mata guda biyu; Inna Galadima, Zarah Bukar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: