Connect with us

WASANNI

Le Roy Zai Cigaba Da Jan Ragamar Tawagar Kasar Togo

Published

on

Hukumar kula da kwallon kafa ta kasar Togo, TFF ta ce mai koyarwa Claude Le Roy, shi ne wanda zai bunkasa kwallon matasan kasar nan gaba kuma tuni ta bashi ragamar cigaba da koyar da ‘yan wasan kasar.

Sabon shugaban hukumar wanda aka sake zaba, Guy Akpobi ne ya bayyana hakan, a lokacin da Le Roy ya sa hannu kan kwantiragin ci gaba da horar da kasar wasa kuma ya bayyana cewa za suyi aiki tare domin cigaban kwallon kafa a kasar.

Koda ya ke ba a bayyana kunshin yarjejeniyar ba, amma watakila kociyan zai ja ragamar Togo zuwa shekara uku nan gaba wanda hakan zaisa ya jagoranci tawagar zuwa wasannin cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa dana duniya.

Wasu na ta caccakar kwazon Le Roy, mai shekara 70, tun bayan da ya karbi aiki a watan Afirilun shekara ta 2016 amma kuma shugaban hukumar kwallon kafar kasar yana ganin zasu sake bashi lokaci domin kawo irin gyaran da yake bukata.

Akpobi ya ce sun bai wa kociyan wa’adin ya kai kasar gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekara ta 2021 da kuma kofin duniya a 2022 wanda kuma duka suna da amannar cewa zaiyi iya yinsa domin cikar wannan buri.

Karkashin mai koyarwa Le Roy, tawagar ‘yan wasan kasar Togo ta kasa kai wa gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a shekara ta 2019 wadda kasar Masar ta dauki bakunci, bayan da kasar ta je ta shekara ta 2017.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: