Connect with us

DAGA NA GABA

Sarkin Gumel Ahmad Muhammad: Gwarzonmu Na Mako

Published

on

Gumel garin Muhammadu Nasoro dan Muhammadu asalin mutanen Gumel Mangawa ne daga Borno. Suna da tarihin kaurace-kaurace da zaman zango a garuruwa daban-daban. Kafin su iso Gumel cikin farkon karni na 19. Wadannan kaurace-kaurace da zango-zango an fara su ne kimanin sama da shekaru dari uku da su ka shude kamar yadda tarihi ya nuna. Ainihin wannan kaura ta samu asali ne sakamakon rashin jituwa a gidan sarautar birnin Gazargamu inda wasu Mainawa suka balle suka yo yamma domin neman wani sabon matsugunni. Guraren da suka zauna shi ne Shaduka da Babayi da Goma tumbi da Malawa kafin su iso Gumel. Mainawan Falki shi ne Muhammadu Didadiga. Danjuma na daya da Danjuma na biyu sune suka sa dan ba ko harsashin farko na samar da kasar Gumel.

 

Sarkin Gumel Ahmad Muhammad

Mai martaba sarkin Gumel Alhaji Ahmad Muhammad Sani Na Biyu CON yana daya daga cikin sarakunan gargajiya na jihar Jigawa mai daraja na daya kuma sarkin da ya fi dadewa akan karagar mulki. Sarki Alhaji Ahmad Muhammad Sani shi ne sarki na sha shida a jerin sarakunan da suka mulki masarautar Gumel . Ya yi fice a cikin sarakunan Jihar Jigawa da arewa baki daya musamman bisa la’akari da irin gudumawar da yake bayarwa wajen ciyar da al’ummarsa da kasa baki daya. Sarkin Gumel ya kasance adalin shugaba abin alfahari wanda a ya nuna kyama ko hantara ga talakawansa. Ya kasance Uba na gari wanda ya dora zuri’arsa akan turba madaidaiciya kuma suna alfahari da hakan. Fadar maimartaba Sarkin Gumel ta shahara wajen karrama baki tare da karfafa musu gwiwa wajen gudanar da kasuwancinsu a masarautarsa. Ya samar da wanzuwar zaman lafiya da taimakawa rayuwar matasa ta hanyar nusar da su don su guji tu’ammali da shaye-shaye da sauran laifuka.

An haifi mai martaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani a watan Disamba .Ya halarci makarantar Elemantare a shekarar 1953 sai makarantar Firamarea 1956 daga nan ya shiga makarantar kwalejin Rumfa da ke Kano 1962. Ya sami nasarar shiga jami’ar Ahmadu Bello Zaria a 1970. Daga bisani ya sami gurbin karo karatu a jami’ar Ohia da ke Amurka a 1976. Inda ya karanci kimiyyar Siyasa ya kammala a 1978. Ya kuma komawa wannan jami’ar don yin digirinsa na biyu. An nada Alhaji Ahmad Muhammad Sani a matsayin sarkin Gumel na goma sha shida a cikin watan disamba a shekarar 1980. Maimartaba sarkin Gumel wajen karbar kyaututtuka iri daban-daban Musamman na gasar tsrean dawaki a gida Najeriya da kuma jamhuriyar Nijar. Wanda kuma shi ne mataimakin shugabanta na din-din-din na kasa.

Alhaji Ahmad Sani ya kasance daya daga cikin ‘yan Najeriya da suka halarci taron tafka muhawara kan siyasa a lokacin tsohon shugaban soji Gen Ibrahim Babangida. Sarkin na Gumel ya taba zama mataimakin amirul Hajj har sau biyu. A shekarar 1994 da 1997. Mai martaba sarkin Gumel y a ba da shawara kan yadda za a kirkiri hukumar kula da iyakoki da shirin sanya yara makaranta.

Sarkin ya taba rike mukamin sakataren jam’iyyar GNPP ta kasa a jamhuriyya ta biyu. A wancan lokaci jam’iyyar ta dora masa alhakin tsara manufofinta ta yadda za su dace da bukatun ‘yan kasa.

A lokacin da yake aiki da hukumar kula da shige da fice ta kasa (immigration ) ya rike mukamin babban jami’I mai kula da zirga-zirga a iyakar gabashin Gamborin gala da a yanzu ke jihar Borno. Ya kuma shugabanci shashin mulki a hedikwatar hukumar da ke Kano.

Ya jagorancin tawagar tsohuwar gwamnatin jihar Jigawa da Kano don halartar taro kan harkar noma a kasar Ghana. Wanda a yanzu jihar Jigawa da Kano ke cin gajiyar abin. Alhaji Ahmad Sani ya kuma kafa hukumar tarihi da al’adu a tsohuwar jahar Kano.

Sarkin na Gumel ya kasance wakili na farko na a makarantar kimiyyar da ke Wudil wanda ke a yanzu ake kira jami’ar kimiyya ta fasaha KUST daga shekarar 1979-1981.

Ya rike mukamin kwamishinan al’amuran cikin gida da yada labarai a gwamnatin tsohuwar jahar Kano ta Marigayi Muhammadu Abubakar Rimi. A lokacin ya sami nasarar kafa gidan jarida na Triumph wanda ke fitar da labarai cikin harshen Hausa da Turanci da Ajami. Ya kuma taimaka wajen kafuwar gidan Talabijin na CTV Wanda a yanzu ake kira da Abubakar Rimi Talabijin (ARTB). Hakan nan kuma ya karfafa nisan zango na gidan Radiyon Kano bangaren FM Da kuma taimakawa yawon bude idanu na garin Bagauda ta Tiga.

Sarki ya kasance jami’I mai kula da tsare-tsare na jahar Kano. Mai kula da yankin Kazaure wajen tabbatar da nasarar kawancen jam’iyyu na GNPP Da PRP a jahar Kano a shekarar 1971 da 1972.

Sarki ya taimaka wajen daga darajar wajen kiwon dabbobi da ke Gumel zuwa na zamani. Ya kaddamar da shirin bankin duniya kan bayar da tallafin bunkasar aikin noma a yankunan karkara. Ya karfafa gwiwa kan muhimmancin da ke tattare ta dashen itatuwa da nufin kare kwararowar Hamada. Ya kuma himmatu wajen nusar da manoma wajen fa’idar shuka amfann gonar da zai samar da abinci ga jama’ar yankin tare da fito da gasar dashen itatuwa a tsakanin hakiman yankin a duk shekara tare da ba wa duk wadanda suka sami nasara kyaututtuka don kyautawa da karfafa musu gwiwa.

Sarkin Gumel ya yi namijin kokari wajen wayar da kan iyaye kan sanya yara a makaranta. Ya sanya idanu kan al’amuran masarautar wadda ta hada da kanannan hukumomi takwas cikin al’amuran da su ka shafi ayyukan.

Allah ya ja da ran Sarkin Gumel Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana, amin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: