Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Fitintinu Sun Mana Yawa, Ga Kuma Firgici, Mece Ce Mafita?

Published

on

Tambaya:

Assalamu Alaykum Akaramakallah, da fatan rubutuna zai zo maka cikin koshin lafiya. In cikin matsala da jarabawa kusan shekara biyu yanzu. Na farko, na dauko wata yarinya na riko, ta gamu da aljanu, ta koma gida, da za ta dawo, ta dawo da jan kaya wai ta sa a jikinta duk ranar lahadi, wai ta samu sauki. Maigidana ya hana ta sa kayan. Bayan kamar wata biyu, muka fita kasuwa, dukanmu muka fita kasuwa sayayya, maigidana ya ga pilowa ya saya, bayan hakan muka fara ganin gashin tsuntsaye a gida. duk lokacin da karenmu ya yi kuka sosai, tabbas za mu kwashe gashin da yawa a gida ranar. Muka shiga addu’a da karanta alkur’ani a cikin gida. Yarana uku duk ‘yanmata, duk safiyar Allah za su tashi da idanunsu jawur, da maigidana. Ni kuma, ina cikin yin azkar dare da rana, abin da suka sa min shi ne firgita da tsoro, a duk lokacin da karenmu ya fara kuka ko da rana ko da dare, sai in kama firgita sosai da kuma ganin wadanan gashin. Muna nan da haka, Allah ya nuna mana pilowan nan da muka saya gashi ne cike da ita. Muka kone ta. Bayan haka ne damuwar ta karu. Gashin ne cikin kayan sawanmu, da na yara, karkashin gadonmu da na yara na, akan gado, cikin mota ne ko ina a gida, hattah net na windodinmu, har a ta abincinmu. Muka bar gidan, inda muka koma, suka biyo mu, kuma duk lokacin da muka shiga kauyenmu, sai su biyo mu gidan kauye. A yanzu dai haka, muna sabon gida, kuma suna nan da mu, a kan kujerunmu, cikin net na windodin gida ne, gashin yana nan. Yanzu ma ciki gare ni na wata shidda. Duk magungunan da zikirori na sunnah, muna ta yi, yarinya mai aljanin kuma har yanzu suna nan da ita, sun sha yin alkawari za su fita amma ba su fita ba, ‘yanmata ne musulmai a jikinta. Ba kuma wanda zai iya gaya mana ga abin da ke damunmu. Mun sha magunguna da na wanka, da hayaki mun gaji. Yanzu dai har, na bar duk magungunan, amma ban bar yin addu’a ba. Akaramakallah, ko za a iya taimaka min da addu’a ko shawarar bi don na samu maganin abubawan da Ikon Allah? Allah ya saka da alkhairi.

 

Amsa:

 

Wa’alaykumussalam. To ‘yar’uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alkur’ani, wasu malaman sun yi bayani cewa: ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta: 117 zuwa ta 122, na suratul A’araf, sai kuma aya ta: 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta: 65-70 a suratu Dhaha, za’a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai.

Sannan ina yi miki wasici da yawan karatun suratul Bakara, saboda muhimmancinta wajan kore shaidanu, kamar yadda ya tabbata a hadisi, kada ki manta da karanta addu’o’in shiga bandaki da na bacci, da azkar na safe da yamma, da kuma tuba daga zunubai, saboda wasu musifun zunubai su ke kawo su.

Idan fitintinun suka cigaba za ku iya mayar da ‘yar rikon, saboda zai iya yiwuwa a tare da ita shu’umcin yake, tun da a baya ba ku ga haka ba, yana daga cikin ka’idojin shari’a, ana tunkude cutar da ta shafi mutane da yawa ta hanyar kau da kai a kan cutar da za ta shafi mutum daya, wannan ya sa mayar da ita bai zai zama laifi ba.

Yana daga cikin hanyoyin tunkude fititinu, nisantar dukiyar haram, in har a kayan gidan da kuke ciki akwai dukiyar da kuka mallaka ta hanyar haram ya wajaba a fitar da ita zuwa mai ita.

Yin sadaka da taimakawa musulmi yana warware mushkiloli, saboda duk wanda ya yayewa wani bakin ciki, Allah zai duba dumuwarsa, hakura da wancan shaidanin karen na ku yana da muhimmanci, saboda mala’iku ba sa shiga cikin gidan da yake akwai kare, kamar yadda ya tabbata a hadisin Bukhari. In har kin bi wadannan shawarwari ina ga za ki samu nasara mai girma.

Allah ne mafi sani.

 

Baffana Yana Yawan Razana A Baccinsa, A Taimaka Mana!

 

Tambaya:

Assalamu alaykum: Mallam ina bukatan shawara ko mafita in Allah yasa kanada masaniya akai.

Kawuna ne ya kasance yakan yi mafarki da dare sai yake razana wani lokaci ya tashi da gudu ko yake kai duka, hakan wlh har yasa yakan ji ciwo sosai.

Kuma ya kanyi addu’o’i kamar karanta Kulhuwa, falaki, Nasi, da ayatul kursiyu amma kuma abun yakan dame shi. Mafarkin nawani kamar macijine kebinsa.

Allah saka da alkhairi ya kuma sa mu samu mafita daga gareku ameen.

 

 

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Duk lokaçın da ya yi mafarki ya razana ya dinga karanta addu’ar da ta tabbata daga Annabi (SAW) a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 3528.

“A uzu bi kalimatillahi tamatan min gadhbihi wa ikabihi wa sharri ibadihi wa min hamazatis shayadini wa anyahduruna”.

In har ya yi tofi sau uku a hagunsa ya canza bangaren kwanciyarsa, ba abin da zai cutar da shi, bayan haka.

Allah ne mafi sani.

 

 

 

 

Yaya Hukuncin Karawa Amarya Yawan Kwanaki, Saboda ‘Honey Moon’?

 

Tambaya:

Assalamu alaikum malam Tambaya meye hukuncin mutumin da yana da mata sai yayi amarya sai yayi mata bisa suka tafi wata kasa wata daya a matsayin honey moon, to meye hukuncin daya matar, ya zalumceta kenan?

 

 

Amsa:

Wa’alaikum assalam To dan’uwa Anas R.A ya rawaito cewa: “Yana daga cikin sunna in mutum ya auri budurwa kuma yana da wata matar, ya yi mata kwana bakwai, in kuma bazawara ce kwana uku” kamar yadda ya zo a Sunanu Attirmizi a hadisi mai lamba ta: 1139, wannan sai ya nuna kari akan haka ya sabawa sunna.

Amma Idan Uwar gida ta bada izni ya halatta ayi kari akan haka, tun da ya halatta mace ta sarayar da hakkinta na kwana, kamar yadda Saudatu ta bawa Nana A’isha kwananta, lokacin da girma ya zo mata, ta ga Annabi (SAW) bai damu da ita ba sosai, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4914, wannan sai ya nuna halaccin sarayar da hakkin kwana, da yiwuwar yiwa amarya kari idan uwar gida ta yarda.

Allah mafi sani.

 

Al’adata Ta Rikice, Saboda Shan Maganin Tsara Iyali, Ya Zan Yi?

 

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Malam don Allah ina da tambaya, don Allah a taimaka min da amsa don kokarin gyara wa Akan lokaci. Malam matsala ta haihuwa greni duk haihuwa ta sai anyi min cs, sai likita ya bani shawarar tsarin iyali don in huta, sai daga nan al’adata Tarikice sai yazo yau bazan sake ganin Shiba sai bayan kwana biyar sai yazo min dayawa, to ni dai wanka na nkeyi nacigaba da ibadata to malam ibadata tayi ko da gyara. Sai kuma da watan Ramadan yazo min dana Kai iya kwankin da yake min wato kwana biyar sai nayi wanka nacigaba da azumi na kuma jinin yana zuwa bai dauke, don sai da yamin wajen kwana goma sannan ya dauke nayi wanka, to shine akace min sai na Rama wannan kwana ki goman shima. To malam ya azumin tawa take.

 

Amsa:

Wa’alaykumussalam To ‘yar’uwa Allah madaukakin sarki a cikin alkur’ani ya rataya hukuncin jinin haila ne da samuwarsa, don haka mutukar kin ga jinin haila da siffofinsa (Baki, ko karni) to ya wajaba ki bar sallah da azumi, har zuwa lokacin da zai dauke, saidai in ya zarce iyaka ta yadda zai zama, yana zubo miki a mafi yawan kwanakin rayuwarki ko dukanta, to a lokacin ne yake zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah da azumi ba.

Duk da cewa tsara iyali ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa “Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Kur’ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911, saidai yawancin magungunan tsara iyali suna birkita al’ada, wannan yasa barin su shi ne ya fi, in ba likita ne ya tabbatar da lalurar shan ba, ko kuma aka gane maganin ba ya cutarwa ta hanyar jarrabawa.

Allah ne mafi sani
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: