Connect with us

RA'AYINMU

Hangen Nesa Game Da Dokar Daidaita Amfani Da Shafukan Sada Zumunta

Published

on

A kwana-kwanan ne, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya sanar da shirye-shiryen da Gwamnatin Tarayya ke yi na daidaita amfani da shafukan sada zumunta a Nijeriya.

Ministan, ya yi wannan furuci ne a gurare daban-daban tare da bayyana hadarin da ke tattare da barazanar rarrabuwar kawuna da cigaban Nijeriya ta hanyar yada labaran karya daga fuskokin da ba a sani ba, wadanda ke amfani da wadannan shafuka na sada zumunta suna cimma manufofinsu, musamman ta fuskar cutar da al’umma da kuma lalata kyaukkyawan dangantakar da ‘yan Nijeriya ke da ita a tsakaninsu.

Haka zalika, wannan kudiri da bangaren zartarwa ke kokarin ganin daidaitawa sahu, ita ma Majalisar Tarayya na yin nata aikin na daidaita amfani da wadannan shafuka na sada zumunta. Domin kuwa, ko a makon da ya gabata Sanatoci sun sake bijiro da sabon kudiri, wanda ke dauke da bukatar aikewa da duk wani wanda ya aikata laifin da ake kira da ‘batanci ga wani ko wata a shafukan sada zumunta’ gidan Yari.

Wannan doka dai an yi mata lakabi da,”dokar bayar da kariya daga shafukan sada zumunta da kuma yi wa wanda bai ji ba, bai gani ba kazafi”, wanda Mohammed Sani Musa ya dauki nauyi daga Jihar Neja, dan asalin Jam’iyyar APC. Kudirin wanda ya tsallake biyawa ta farko da ta biyu a Majalisar ranar Talatar da ta gabata, ta yi nuni da tara ko dauri ko kuma duk biyun na Naira 150,000 ga duk wanda aka samu da aikata wannan laifi. Inda kuma dokar ta ayyana cin tarar Kamfanunnukan Yada Labarai makudan kudaden da suka tasamma Naira Milyan 10, wajen yada labaran karya ko kuma kawo labaran da za su sanya mutane cikin rudani.

Sanata Musa, ya bayyana cewa ko shakka babu akwai bukatar wannan doka a wannan kasa tamu, “idan kasashe irin su Philippines, Singapore, Italy, Malaysia, Australia, France, Indonesia da kuma Egypt za su yi kokarin dakile yada labaran karya da farfaganda, me zai hana mu mu ma aiwatar da hakan?”

“Tunda aka kafa Nijeriya, ba ta taba samun kanta a hali na rarrabuwar kai irin wannan lokaci ba”, ya kara da cewa, wannan doka ba wai tana son hana mutane yin amfani da shafukan yada zumunta ba ne, illa dai kawai hana su rika yada labaran da ba na gaskiya bad a sauran masu alaka da farfaganda.”

Musa ya cigaba da cewa, kasashen da suka cigaba su ma sun fuskanci irin wannan kalubale a daidai nasu lokacin, amma sun samu nasarar dakile al’amarin ta hanyar yin amfani da dokokin da suka dace. “Don haka, ya zama wajibi a yi duk mai yiwuwa tare da mayar da hankali wajen daidai amfani da shafukan sada zumunta a Nijerya”, a cewar tasa.

Kodayake dai, wannan kokari na kawo daidaito a shafukan na sada zumunta ya janyo cece-kuce a tsakanin wasu ‘yan Nijeriya, ciki har da wani Babban Limamin Kiristoci daga Jihar Sakkwato, Rebaran Matthew Kukah. Wanda ya kalubalanci wannan kudiri na Gwamnatin Tarayya kan kawo daidaito a shafukan sada zumunta, domin shi a nasa ganin wannan wata hanya ce da ake son bijiro da ita don hana ‘yan Nijeriya fadin albarkacin bakinsu. Kuka, ya bayyana haka ne a wajen wani taro da aka yi a Jami’ar Owo da ke Jihar Ondo kwanan nan.

Ya kara da cewa, kafafen sada zumunta wasu zauruka ne wadanda ke baiwa ‘yan Nijeriya damar fadin albarkacin bakinsu da sauran abubuwan da ke damunsu wanda ya shafi kasa, sannan ya kara da cewa, ya fahimci wasu Shugabani na yanzu ba su ma san cewa, gwagwarmayar da su ke yi akan ‘yan Nijeriya ta yakar demokradiyya ce da kuma hana su fadin albarkacin bakinsu ba.

Haka nan, ita ma Jam’iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci wannan kudiri na gwamnati, inda ta daga wa Jam’iyyar APC yatsa wadda ke mulkar tarayyar Nijeriya tare da zargin ta da cewa, kawai ta son kawo rudani ne ta hanyar hana al’ummar Nijeriya amfanuwa da damar dokar kasa ta ba sun a fadin albarkacin baki da kuma abubuwan da ke damun su.

Jam’iyyar ta PDP ta gargadin cewa, wannan kudiri da gwamnati ke yunkurin aiwatarwa ba komai ba ne, illa yunkurin canza dokar kasa tare da yi mata kwaskwarima a dakile wa mutane damar da demokradiyya ta ba su ta hanyar tsarin dokokin kasa da kuma lalata cigaban kasar kacokan.

Sannan PDP, ta sake bayyana wannan kudiri a matsayin wata hanya ta yi wa ‘yan Nijeriya mulkin kama-karya tare da tauye musu hakkunansu na fadin abubuwan da ke damun su, fadin ra’ayoyinsu da kuma tattaunawa a tsakaninsu.

Babu shakka, wannan Gidan Jarida na goyon bayan wannan kudiri na daidaita amfani da shafukan sada zumunta. Sannan ya zama wajibi a dauki matakan gaggawa kan yada ire-iren labaran karya da batanci, wadanda ke haifar da fitintinu a tsakanin al’ummar wannan kasa.

Haka nan, ya kyautu gwamnati ta yi la’akari da maganganun bangaren ‘yan adawa ta fuskar bijiro da dokoki wadanda ba za su wancakalar ko hanawa al’ummar wannan kasa damar da dokar kasa ta ba su ba, musamman a bangaren fadin albarkacin bakinsu da ra’ayoyinsu da kuma abubuwan da ke damunsu ba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: