Connect with us

Hannunka Mai Sanda

Me Ya Sa Masu Kare Hakkin Dan Adam Suka Yi Gum Da Batun Sace Yaran Kano?

Published

on

A ci gaba da kalubalantar masu da’awar karajin kare hakkin Dan’adam a baki, wadanda tasirin kabilanci da addini ke sanya su kin yi wa wadanda ba ‘yan bangarensu adalci ba, Kungiyar ta Muric, ta gabatar da wasu bayanai na raddi da tuhuma a kansu, da Harshen Ingilishi, a cikin da yawan manyan Jaridun wannan Kasa.

A baya can, mun tsaya ne a wata gaba da Kungiyar ta Muric ta gabatar da wasu bayanai cikin Harshen Nasaru, wanda ba a fasaara ba. Ga fassarar;

“… Hakika ‘yanNajeriya za su iya tuna babatu (da irin wadancan Kungiyoyi na-buge, dake da’awar kare hakkin Dan’adam bisa asasi na kabilanci) da ya biyo baya, ba tare da kakkautawa ba, game da lamarin Ese Oruru (wata “yar mutan Kudu, da ta biyo Saurayinta Arewacin wannan Kasa, bisa radin-kanta, da burin ya aure ta, amma a karshen lamari aka birkita maganar) da ya afku a Watan Mac, na Shekarar 2016 (March, 2016)…….

(Gashi a Kano an sace daruruwan kananan Yara. Gasu Musulmai ne, amma sai aka mayar da su Kiristoci. Sannan, a karshe aka sayar da su ga masu cin-kasuwar Mutane. Saboda haka)…Ina irin wadancan Kungiyoyi dake riya kumajin kare hakkin Kananan Yara, wadanda lokacin da ake cikin jimurdar lamarin Ese Oruru (sai suka zamto) tamkar su fado da sama kasa saboda babatunsu, cikin sha’anin da kawai, wasu ne suka gudu, bisa dalilin son aurar junansu. Sannan kuma, shin, wai yanzu ina Lauyoyin dake da’awar kare hakkin Dan’adam suke a yau (me suka yi, ko suke kokarin yi, game da Yaran Musulmi, da Inyamurai-Kiristoci suka sace a jihar Kano) ?”.

Kungiyar ta Muric, ta cigaba da cewa;

“…The hijab controversy has been raging in the Southwest for ober three years now, and they are yet to find their boice. They habe refused to speak up for millions of female Muslims children who habe been repressed. Many of them habe been forced out of Schools and our human rights actibists beliebe it is business as usual”.

Ga fassarar Turancin na bisa kamar haka;

“… Sanin kowane cewa, an yi matukar gwaggwama nunfarfashi game da batun sanya hijabi sama da Shekaru uku, a yankin Kudu-maso-yamma na wannan Kasa, amma shiru kake ji, irin wadancan Kungiyoyi na kare hakkin Dan’adam ko uffan ba su ce ba game da danbarwar. Sun yi gum da bakunansu, a lokacin da ake tauye hakkin miliyoyin ‘yanMata Musulmi. Da yawan irin wadancan ‘yanmata, an kore su ne daga Makarantu (wai fa, laifinsu shi ne, sanya hijabi. Alhali kowa cikin Kasar, na da damar dabbaka irin kalar Addinin da ya zaba ya darje), amma sai irin wadancan Kungiyoyi dake da’awar kare hakkin na Dan’adam suka nuna ko-a-jikinsu, tamkar irin wannan tauye hakkin ba wata matsala ba ce abar la’akari”.

Ayar-tambaya (?) Ga Shugaban Amurka Trump Game Da Batun Sace Yaran Kanawa A Kano

Ba ya ga irin wadancan Kungiyoyi na Kare Hakkin Dan’adam na fatar-baki, da ake da su a nan Nijeriya, wadanda Kungiyar Muric ke ganin-beke game da rashin nuna damuwarsu da batun sace Yaran Kanawa da Inyamurai-Kiristoci suka yi a Kano, Kungiyar, ta kalli Shugaban Amurka, Donald Trump, tare da gabatar masa da ayar-tambaya (?) kamar haka;

“…We’re not surprised that, the kuestion on the lips of President Donald Trump is always “why are you killing Christians in Nigeria?”. Trump will neber ask, “why are you persecuting Muslims girls in Nigeria?”…”

Ga fassarar kalaman Kungiyar ta Muric cikin Harshen Hausa;

“…Ko kadan ba mu yi mamakin babatun da kullum za a ji Shugaba Trump na yi ba cewa, “mai yasa ne kullum kuke kashe Kiristoci a Najeriya?”. Sai gashi daidai da minti guda ba a taba jin sa na cewa, “me yasa kuke uzzirawa “Yan Mata Musulmi a Najeriya?”…”.

“We call on justice-lobing Americans to speak up!!!”

“…Mu na kira da babbar murya ga Amurkawan dake da muradin ganin a na kamanta adalci, da su daure su ce wani abu (game da batun sace Yaran na Kanawa)”.

In ji Kungiyar Muric.

A karshen kalaman Kungiyar ta Muric, wadanda suka fito a takardun manema labarai da Kungiyar ta fitar, karkashin kulawar Farfesa Ishak Akintola, daraktan Kungiyar, za a ga sun yi kira hatta ga Majalisar Dinkin Duniya, da ta ce wani abu, game da mummunan tauye hakkin “yan mata, a matsayinsu na bani-adama, sannan kuma mabiya addinin musulunci da ake ta kan yi cikin wannan Kasa ta Najeriya a yau.

Ba Kungiyar Muric ce kawai ta yi korafi game da wadanda suka sanyawa bakunansu linzami ba game da irin wannan mummunan alkaba’i da ya faru ga Yaran na Kanawa ba, babu shakka akwai ma wasu daidaikun Mutane gami da Kungiyoyi da suka nuna takaicinsu game da ta’adar ta yin gummm!!!

Gidajen Talabijin Na AIT da TVC da Channels TV Duka Sun Yi Lakur Game Da Yaran Kanawa Da A Ka Sace

Masharhanta sun ga beken wadancan gidajen Talabijin da aka lasafta a sama, duba da shiru ko mukus da suka yi, a lokacin da ake kan ganiyar batun Yaran Kanawa da Inyamurai-Kiristoci suka yi awon-gaba da su, zuwa yankin Kudu-maso-gabas na wannan Kasa, a matsayin wadanda aka sace, a ka raba su da iyayensu, da garinsu, da danginsu, kai har ma da addininsu. Kamar yadda bayanai suka jima da fitowa cewa, bayan sace yaran na al’umar Musulmi, a karshe kuma a kan canja musu akalarsu ne daga Addinin Musulunci zuwa ga Addinin Kiristanci. Duk da cewa irin wannan jirkitar da Mutum ta-karfi zuwa ga wani Addini, haramun ne a litafan mabanbantan Addinai, kai!!! Hatta ma ko da za a duba Kundin Tsarin Mulkin Kasa, aikata hakan haramun ne.

 

A cikin irin wadancan gidajen Talabijin da aka ambata a sama, za a ga a koda yaushe wani dan karamin abu ya afku na rashin jin dadi, musamman tsakanin mutumin Arewa da mutumin Kudu, nan da nan ne za a ji babatunsu, suna ta antayo bakaken kalaman da mai saurare zai yi tunanin, kafin ya je Umarah ya dawo, Najeriya na iya tarwatsewa. To amma sai gashi irin wannan babban abu na cutarwa ga jama’ar Kano Musulmi ya faru, amma sai suka ki tofa albarkacin bakinsu a kan lokaci, kamar yadda suka saba.

Ina Femi Kayode (FFK), Ina Remo Omokri, Ina Prof. Chidi Odin Kalu Da Ire-irensu?

Duka wadancan mutane da ake cigiyarsu, sun saba yawaita maganganu tuli, masu ma’ana da akasinsu a Kasa, musamman bisa asasin bangarenci ko kabilanci ko addini. Sai dai kusan a kullum, suna masu kare yankin Kudancin Kasar ne. Amma game da sace Yaran Kano kuwa, duka sai suka yi duma, suka ki cewa uffan!.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: