Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din Wazeer

Published

on

Suna: Wazeer.

Labari: Al’ameen Buhari.

Tsara labari: Al’ameen Buhari.

Kamfani: 3SP International Ltd and ABCL Company Ltd.

Daukar Nauyi: ABCL Company Ltd.

Shiryawa: Auwal Sani.

Bada Umarni: Abubakar S. Shehu.

Sharhi: Musa Ishak Muhammad.

Jarumai: Ali Nuhu, Shu’aibu Lawan Kumurchi, Al’ameen Buhari, Tijjani Faraga, Sadik Ahmad, Abubakar S. Shehu, Abubakar Kaita, Hafsat Idris, Zainab Ishola da sauransu.

 

Fim dinWazeer, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani magidanci mai suna Wazeer (Ali Nuhu), wanda a ke zargi da kisan matarsa A’isha. Ita dai A’isha mace ce mai dukiya, domin kuwa shi kansa Wazeer dinya na aiki ne a karkashinta.

 

A farkon fim din dai an nuna ‘yan sanda sun samu labarin rasuwar Hajiya A’isha, wadda a ka shigo har gidanta a ka kashe ta ta hanyar soka mata wuka. Nan take ‘yan sanda su ka shiga bincike karkashin jagorancin(Shu’aibu Lawan Kumurchi). A haka dai bincike ya yi bincike har magana ta isa zuwa gaban kotu. A shirye-shiryen da Wazeer ya ke na fuskantar shari’a, Lauya dinsa ya bashi shawarar gayyato wata babbar lauya mai suna Khadija(Hafsat Idris) saboda kwarewar da ta ke da shi a fannin Shari’a. Bayan sun amince da karbar wannan shari’a, sai Barrister Khadija da mataimakinta Barrister Hamza (Sadik Ahmad) su ka zo domin tunkurar shari’ar.

A haka dai a ka fara zaman shari’a kamar yadda kotu ta tsara. Sai dai tun kafun a Fara shari’a, Barrister Hamza ya fadawa Barrister Khadija cewa shi fa bai gama yarda da Wazeer ba, kuma ya na zargin ma shi ne ya kashe matarsa da kansa. Sai dai Barrister Khadija ta yi wa Wazeer gargadinficewa daga shari’ar idan har ta fahimci ya boye mata wani abu game da shari’ar. A haka dai a ka gama zama na farko da na biyu, amma bangaren hukumar ‘,yan sanda da gwamnati, ba su iya samun gamsassun hujjojin da za su iya tabbatar da cewa Wazeer shi ya kashe matarsa A’isha.

A zama na uku, kotu ta wanke Wazeer daga zargin kisan da a ke masa, kuma nan take kotu ta bada umarnin a sake shi, kuma ta kori karar daga gabanta. Bayan an kori karar ne Kuma, wata rana Barrister Khadija ta zo gidan Wazeer, saboda sun fara soyayya a zaman shari’ar da su ka yi. A zuwan ta gidan ne, sai ta yi kacibus da wasu takardu wadanda su ke nuna mata cewa tabbas Wazeer ba shi da gaskiya kuma shi ya kashe matarsa da kansa. Nan take ta fito daga gidan da gudu, ta kirawo yan sanda ta sanar da su komai, sannan ta nemi su taimaka mata, saboda rayuwarta ta na cikin hatsari. Haka kuwa a ka yi sun je sun cece ta bayan Wazeer ya zo ya dauke ta ya kai ta daji domin ya kashe ta, sai dai yan sanda sun harbe shi nan take kuma ya fadi ya mutu.

ABUBUWAN YABAWA.

 

  1. Fim din ya samu aiki mai kyau matuka, daga masu shiryawa da bada umarni, har ma da jaruman da su ka taka rawa a cikin fim din.

  2. Sunan fim dinya dace da fim din.

  3. Labarin bai yanke ba tun daga farko har karshensa.

  4. Sauti da hotuna sun futa radau.

  5. An nuna muhimmancin hujjoji kafun iya tabbatar da laifi ga mai laifi a kotu, kamar yadda ya faru a kan Wazeer.

KURAKURAI

  1. An nuna lokacin da Wazeer ya kashe A’isha su kadai a gidan daga shi sai ita, to wa ne ne ya samu labarin kisan har ya sanar da ‘yan sanda?

  2. Takardar da Barrister Khadija ta gani dakin Wazeer, ba ta Isa gamsar da ita cewa Wazeer ne ya kashe A’isha ba, amma daga ganin takardar sai ta fice ta na sanar da ASP cewa Wazeer ne ya kashe A’isha.

  3. Duk da girman arzikin Hajiya da kuma girman gidan da su ke zaune ita da Wazeer, amma babu mai gadi a gidan, kuma babu mai aiki ko daya a gidan.

  4. Ya ya a ka yi ‘yan sanda su ka san Wazeer ya dauke Barrister Khadija ya gudu da ita daji, har su ka zo ceton ta.

  5. A lokacin da Barrister Lukman ya ke gabatar da Barrister Khadija da Barrister Hamza ga Wazeer, ya ce sunan wannan Barrister Hamza Abubakar, amma a rubutun turancin da a ke yowa a kasa sai a ka rubuta Barrister Hamza B. Umar.

KARKAREWA

Fim dinWazeer fim ne da ya samu nasarori sosai, musamman wajen jan hankalin mai kallo tun daga farko har karshe. Kuma fim dinya kayatar sosai, duk da an dan samu kurakurai kadan, amma tabbas nasarorin fim dinsun fi kalubalensa yawa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: