Connect with us

Uncategorized

Zargin Yunkurin Lalata Da daliba- Kwalejin Kadpoly Ta Kore Malami

Published

on

Mahukuntan Kwalejin Fasaha da Kimiyya dake a jhihar Kaduna wato KadPoly ta kori tsohon Shugaban daya da cikin Sashen sa Kwalejin bisa zargin yunkurin lalat wata daliba yar Kwalejin.
Shugaban wanda aka sakaya sunan sa, mahukuntan Kwalejin sun amince da korar sa ne a taron da suka yi karo na 91 a ranar 30 ga watan Janirun shekarar 2020.
Korar tsohon shugaban tana kunshe ne a cikin wata wasikar da Mataimakin Mahutin Kwalejin Samuel Y. Obochi ya baiwa jaridar Daily Trust a Kaduna.
A cewar wasikar, mahukuntan sun dauki matakin korarar tsohon shugaban ne bayan da dalibar ta kai rahoto ga mahukuntan Kwalejin,inda hakan ya sanya mahukuntan Kwalejin suka gayyace don ya gurfana a gaban mahukuntan da kuma kwamitin ladabtarwa don ya yi bayani kan zargin da ake yi masa.
A cikin sanarwar Shugaban Kwalejin Farfesa Idris M. Bugaje, a watan Disambar shekarar 2019 ya kaddamar tsari akan haramta dukkan wani abu day a shifi yin badala ko kuma yiwa mata dalibai barazar son yi lata dasu a Kwalejin.
A karshe Shugaban Kwalejin Farfesa Idris M. Bugaje ya gargadin cewar, mahukuntan Kwalejin baza ta lamunci dukkan wasu nau’ukan badala daga gun malaman Kwalejin ba, inda ya shawarci masu ruwa da tsaki dasu tabbatar da suna bin dokokin da mahukutan Kwalejin suka gindya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: