Connect with us

RIGAR 'YANCI

Al’ummar Tarauni Na Godiya Ga Wakilinsu

Published

on

Dimukradiyya ce dandamalin da jama’a ke yi wa masu bukatar dafe kujerun iko kallon tsanaki, domin zavar wadanda suke da yakinin kwallaliya za ta biya kudin sabulu, hakan tasa al’ummar Karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano, suka yada kwallon mongwaro domin hutawa da kuda, inda a zaven shekara ta 2019 na Wakilin Majalisar Wakilai ta tarayya, suka gwammace zavar matashi mai kishin cigaban al’ummar yankin, domin maye gurbin wanda su ka yanke tsammanin samun tagomashin romon demokradiyya daga gare shi, bayan shafe shekaru ya na wakiltar al’ummar Karamar Hukumar Tarauni a majalisar wakilai ta tarayya.

Hon. Hafizu Ibrahim Kawu, shi ne wanda ya yi hafzi da ruwan kuri’un al’ummar Karamar Hukumar Tarauni, inda ya yi wa tsohon wakilin da ke kan kujerar a baya fintikau, wajen samun kuri’un da suka ba shi damar wakiltar al’ummar Tarauni a wannan karon. Alhamdulillahi, kwalliya na biyan kudin sabulu, kasancewar  Alhaji Hafiz Ibrahim Kawu shi ne wakilin da ba a tava samun wakili da ya bujiro da abubuwan mamaki wadanda su ka tabbatar da nagartarsa da kuma kyakkyawar biyayya ga Shugabancin Jam’iyya.

A karon farko a Jihar Kano, shi ne wakilin da ya bude wa kowacce Mazava Ofishin Jam’iyya, wanda jama’a ke samun zuwa domin kai korafe-korafensu domin gabatar wa da wakilin nasu a Majalisar Wakilai ta Tarayya, wannan ko shakka babu ya kara kusanta jama’a da wakilinsu. Sannan kuma, ya yi kokarin bujiro da sabbin tsare-tsaren da a halin yanzu suka zama Zakaran-gwajin-dafi, musamman shirinsa na koyar da mata masu shekara 18 zuwa sama, sana’ar daukar hoto.

Babu shakka, sabbin tsare-tsare wanda wannan nagartaccen wakili ya zo da su ne yanzu ke kanshin turare dan goma, domin kuwa yanzu haka ya samar wa sama da Matasa 100 ayyukan yi, baya ga koyar da sana’o’i iri daban-daban da a halin yanzu al’ummar yankin ke sharvar romon demokradiyya tare da yin godiya da wanan kyakkyawan wakili.

Sai kuma, babban al’amarin da yake daukar hankalin duk wani wanda ya kwana kuma ya tashi a wannan Karamar Hukuma, ganin yadda duk makon duniya matukar Hafiz Kawu na Kasa, za ka tarar da shi ya shigo Karamar Hukumarsa ta Tarauni, domin ganawa da jama’a tare da sauraron bayanan irin abubuwan cigaban da suke bukata a yankunansu.

Alhaji Talle Mai Unguwa, shi ne jagoran Jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Tarauni, da yake yi wa Jaridar Leadership A Yau karin haske kan nasarorin da aka cimma daga lokacin da aka rantsar da Hafizu Kawu akan wanna kujera cewa ya yi, ko shakka babu al’amarin wannan wakili akwai ban sha’awa, musamman kishinsa ga cigaban al’umma da kuma kyakkyawar biyayyarsa ga Jam’iyya,  “mun gamsu kwarai da gaske da tsarin wakilcinsa, kuma mu na yin alfahari da shi, sannan kuma ba ma nadamar zavarsa, domin al’ummar wannan yanki ba za su manta da irin ayar da aka gasawa al’umma a hannu ba daga vangaren tsohon wakilin da ya gabata.

Haka zalika, Hafiz Ibrahim Kawu na shirin hada karfi da Abokan aikinsa a Majalisar Wakilai, domin tunkarar yadda za a inganta harkokin makarantun tsangayu da kuma yadda za a tallafawa harkar Karatun Alkur’ani ta yadda zai tafi kamar yadda zamani yake kai a yanzu da kuma samar da kykkyawan tsarin magance matsalar barace-barace da ke addabar Arewacin Kasar nan.

Domin ji daga vangaren wakilin na Karamar Hukumar Tarauni a Majalisar Tarayya, Hafiz Ibrahim Kawu ya bayyana nasarar da Gwamna Ganduje ya samu a Kotun Koli da cewa, nasarar ta al’ummar Jihar Kano ce baki-daya, sannan kuma ya yi tsokaci kan irin nasarorin da ya samu zuwansa kan wanna kujera da cewa, kamata ya yi duk wanda jama’a su ka zava ya zama shi ne zai yi wa al’ummar hidima ba wai ya zuba ido sai dai a yi masa ba. Haka kuma, ni abinda na dauka wajibi ne yi wa jama’a aiki kamar yadda dokar kasa ta ba shi dama, tare da yin kokarin kare kima da mutuncin al’ummar da ya ke wakilta, in ji shi.

A karshe, Kawu ya godewa al’ummar Tarauni bisa kyakkyawar fahimtar da suke nunawa wakilcin nasa, daga nan sai ya yi alkawarin cigaba da kwararowa al’ummar yankin ayyukan raya kasa tare da yin duk mai yiwuwa wajen sama wa Matasa aikin yi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: