Connect with us

RIGAR 'YANCI

Matar Gwamnan Nasarawa Ta Zage Damtse Wajen Tallafa Wa Marayu

Published

on

Uwargidan Gwamnan jihar Nasarawa, Hajiya Farida Abdullahi Sule, ta zage karfinta wajen ganin ‘ya’yan marasa galihu, don ganin sun zama tamkar ‘ya’yan masu hannu da shuni.

Matar Gwamnan ta dukufa wajen taimaka wa rayuwar almajirai marasa galihu masu fatan Allah ya ba ku mu samu.

Tun da a ka rantsar da Injiniya Abdullahi Sule, bisa karagar mulkin jihar Nasarawa, matarsa, Amarya Farida Sule ta dukufa wajen ganin ta ceto rayuwar  ‘ya’yan talakawa daga kangin wahala.

Uwargidan gwamnan ta kasance ta na bauta wa nakassasu marasa galihu ta hanyoyi daba-daban.

Cikin taimakon da ta ke yi wa ‘ya’yan talakawan musamman wadanda ke rayuwa cikin kunci.

Ta kan agaza masu da abubuwan more rayuwa na jin dadi wanda kowane yaro ya ke fatan ganin iyayen sa sun yi ma sa.

A kwankin baya, Farida Sule ta rika hidima ga ‘ya’yan Talakawa marasa galihu da ke karatu a Makarantar Nakasassu, da ke garin Lafia.

Wannan taimakawar da ta ke yi ya sanya ta samu lambar yabo mai girma daga hukumar kula da Makarantar (special schools).

Baya ga wannan, Hajiya Farida Abdullahi Sule, ta rungumi almajirai masu fatan Allah ya ba Ku mu samu. inda ta cigaba da ziyartan makarantun allo ta na taimaka wa almajirai da kayan masarufi.

Ta ziyarci makarantar Allo na Malam Atiku da na Malam Sabo Baba, da kuma wasu masu yawa, cikin ziyartan ta Makarantun allon wasu makarantun ta raba wa almajirai sama da 200 kayan Sallah.

Sannan ta raba kayan abinci da sauran su. Haka-zalika takan agaza wa wadanda rayuwarsu ta nakasa.

Hajiya Farida Abdullahi Sule, ta kasance mai yawan ziyara ga gidajen Marayu lokaci bayan lokaci.

Hajiya Farida Abdullahi Sule, ita ta fara ziyartan sabon gidan marayu da a ka bude a Lafia, hawan su mulki ke da wuya yana cikin ayyukan ta na farko ta ziyarci gidan ta kuma tafi da tarin kyaututtuka zuwa ga marayun da babu uwa babu uba, yara kanana.

Hakaza-zalika a lokacin bikin murnar ranar haihuwan Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, Hajiya Farida ta shirya gagarumin biki wanda aka yi shi a gidan marayun wanda ya samu halartan Gwamnan jihar da dukkanin mukarraban Gwamnatin jihar.

A wannan bikin ne Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, tare da Hajiya Farida da sauran al’umma suka ci abinci iri daya da marayun da ke gidan. Bayan haka, ta raba kayan abinci da na marmari da sauran kayan masarufi.

Hajiya Farida Abdullahi Sule ta na taka mahimmiyar rawa wajen gina ilimin yara kanana musamman marasa galihu, hakan ya sanya ta samu lambar yabo masu yawa a gurin sarakuna da Mahukuntan Manyan makarantu.

Sannan ta na ziyartar Babban Asibitin garin Akwanga da ke Nasarawa ta Arewa, inda ta sanya aka rika duba marasa lafiya a kyauta. ta kuma ba su agaji na musamman. Saboda kwazonta,  Masarautan  Karshi ta girmama Hajiya Farida Abdullahi Sule, da sarautan Innawuron Karshin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: