Connect with us

RAHOTANNI

Nijeriya Ta Bude Sabon Babi Na Bayar Da Biza Domin Saukaka Hada-Hadar Kasuwanci

Published

on

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon Kundin Tsare-tsaren Bayar da Biza na Shekarar 2020 a fadarsa da ke Abuja, a hukumance.

Wadanda suka shaidi kaddamarwar sun hada da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ministan cikin gida Ogbeni Rauf Argebesola, ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed, babbar sakatariyar ma’aikatar cikin gida Barista Georgina Ekeoma Ehuriah, shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) Muhammad Babandede.

Sauran sun hada da babban mai bai wa shugaban shawara a kan yada labarai Femi Adesina, shugaban kwamitin harkokin cikin gida a majalisar dattawa Sanata Kashim Ibrahim Shettima da takwararsa na majalisar wakilai Hon. Nasiru Sani Zangon-Daura da sauran wakilai daga ma’aikatar cikin gida da hukumar shige da fice.

Sabon Kundin Bayar da Bizar ya bude sabon babi game da sababbin matakan da za a rika bayar da bizar a kansu saboda bunkasa hada-hadar kasuwancin kasa.

Sabon Kundin Tsarin Bizar na Nijeriya da aka fadada, an samar da shi ne bayan rattaba hannu a kan yarjejeniyar sakin-marar kasuwanci ta Nahiyar Afirka, wacce ta bude kofofin kasuwanci da ‘yancin kai-komon jama’a a tsakanin kasashen da suke da karfin tattalin arziki a nahiyar.

Sanarwar manema labarai da Shugaban NIS Muhammad Babandede ya fitar a ranar Talata, ta yi bayanin cewa, Babban makasudin da ya sa aka yi sauye-sauyen da suka kai ga samar da Kundin Bizar na 2020 shi ne domin karfafa matsayin Nijeriya na kasancewarta Giwar Afirka ta fuskar ci gaban tattalin arziki ta hanyar kara janyo hankulan masu zuba jari na kasar waje zuwa cikin kasar, wanda zai bude hanyoyin samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa da tsamar da su daga kangin talauci, dai-dai da kudirin Shugaba Buhari na raba ‘Yan Nijeriya akalla miliyan 100 da talauci nan da shekara 10.

Wakazalika, an tsara kundin ne ta yadda zai taimaka wa shirin farfado da tattalin arziki da bunkasa ci gaba a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020, kuma har ila yau zai kasance wata hanya ta cimma kudirin gwamnati mai ci a yanzu na inganta tsaron kasa da cigaban tattalin arziki da tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Sanarwar wacce ta zo ta hannun jami’in yada labaru na NIS, DCI Sunday James ta kara da cewa, da yake jawabi a yayin kaddamar da sabon kundin na biza a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ministan cikin gida Ogebeni Rauf Aregbesola ya bayyana muhimmancin kundin a matsayin kashin bayan saukaka hada-hadar kasuwanci a Nijeriya.

Ya kara da cewa, ana sa rai sabon tsarin na biza ya bunkasa cigaban tattalin arziki musamman ta sashen yawon bude, sufurin jiragen sama, nishadantarwa, cinikayya da sauran sassan da Nijeriya take da tagomashi fiye da sauran takwarorinta na Afirka. Har ila yau, kundin zai kuma bai wa Nijeriya damar kara yaukaka zumunci a tsakaninta da takwarorinta.

A cewarsa, “Sabon Kundin Tsare-tsaren Bayar da Biza na shekarar 2020, ya bullo da sababbin tsare-tsaren bayar da izinin shiga kasa ga ‘Yan Nijeriya da ke kasashen waje wadanda suka zama ‘yan kasa ko dai ta sababin haihuwarsu a cikin kasa , ko aure ko kuma cike ka’ida domin su rika sauke nauyinsu a matsayin ‘yan kasa. A halin yanzu Irin wadannan ‘Yan Nijeriyan suna da damar su yi amfani da fasfon kasar da ta amshe su a matsayin ‘ya’yanta su shigo Nijeriya ba tare da sai an ba su takardar takaitaccen izinin zama a kasa ba,” in ji shi.

Ministan ya bayyana dukufar da ma’aikar cikin gida ta yi wajen aiwatar da kundin a aikace bisa nauyin da ke wuyanta na duba ayyukan Hukumar NIS.

Ogbeni Rauf Aregbesola ya tabbatar wa da ‘Yan Nijeriya cewa NIS za ta yi aiki da tsare-tsaren kundin bizar ta hanyar nuna kwarewar aiki da tabbatar da gaskiya da rikon amana kuma a kan lokaci. Ya kara da cewa hukumar ta shige da fice za ta zuba jari mai kaurin gaske wajen horas da jami’anta da za su yi aikin bayar da bizar a cibiyoyin NIS da kuma ofisoshinta na sassan shiga kasa.

Ministan ya kara da cewa, NIS za ta kuma yi aiki da dukkan masu ruwa da tsaki a ciki da wajen kasar nan domin tabbatar da cewa ba a saba ka’ida wajen aiki da sabon kundin bizar ba da kuma sakaci da tsaron Nijeriya ko wasu kasashen da za su ci gajiyar abin.

“Aiki da sabon kundin ba zai sa a yi sakaci da tsaron kasa ba, kasancewar an dauki kwararan matakai na tantancewa tun kafin a shigo cikin kasa da kuma bayan an shigo,” ministan ya jaddada.

Da yake karfafa ‘Yan Nijeriya mazauna ketare su girmama dokokin shige da fice na sabbin kasashensu da kuma na Nijeriya, ministan ya taya Hukumar NIS murnar gagarumar nasarar da ta samu a kan sabon kundin bizar, kana ya gayyaci masu zuba jari da masu ziyara su yi kokarin cin gajiyar sabon babin da Nijeriya ta bude ta hannun hukumar shige da fice.

“Aiki da sabon kundin bizar na shekarar 2020 zai bukaci a samu hadin gwiwa da ma’aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban ta fuskar difilomasiyya, kasuwanci, zuba jari, ilimi, yawon bude ido, ayyukan masana’antu, manufofin kudi, tsaro, tattara bayanan sirri da sauran abubuwa da dama,” in ji ministan.

Wasu daga cikin tanade-tanaden kundin bizar na shekarar 2020 sun hada da tsarin bayar da biza ga ‘yan kasashen da ke cikin Kungiyar Hadin Kan Afirka, da kara yawan matakan biza daga shida (6) zuwa saba’in da tara (79), da samar da lambar shaida ga kowane mataki na biza da kuma samar da tsarin bayar da biza ta shafin intanet.

Sanarwar ta shugaban NIS Muhammad Babandede ta kuma yi bayanin cewa alfanun sabon kundin bizar na shekarar 2020 suna da daman gaske, kasancewar ya samar da damammaki ga Nijeriya na zama babbar cibiyar zuba jari a Afirka, da karbar bakuncin manyan tarurruka da bukukuwa na duniya musamman wadanda aka kebe gudunar da su a Afirka. Har ila yau, kundin zai kasance kashin bayan bunkasa sashen sufurin jiragen sama na kasa, da bangaren masana’antun wasannin nishadi da yawon bude ido.

Bugu da kari, ana sa ran sabon kundin bizar ya daukaka matsayin Nijeriya a rahoton nazarin saukaka bayar da biza wanda Bankin Bunkasa Cigaban Afirka (AFDB) ke wallafawa duk shekara, inda hakan zai kara wa Nijeriya tagomashi a jadawalin kasashen da suka fi saukaka hada-gadar kasuwanci a duniya.

Shi kuwa Shugaban NIS Muhammad Babandede, a yayin kaddamarwar, ya yi bayani ne game da abubuwan da suka kebanci sabon kundin tsare-tsaren bayar da bizar na shekarar 2020 da kuma karin haske a kan kudurorin da ake son cimmawa da sabon kundin, da amfaninsa da matakan da ya kunsa tare da jaddada yadda za a yi aiki da kundin ba tare da an yi sakaci da batun tsaron cikin gida ba

Za a iya cewa dai wannan sabon kundi na tsare-tsaren bizar Nijeriya na shekarar 2020, ya bude sabon babi ga kokarin cimma manufar bunkasa tattalin arzikin kasa domin kyautata jindadi da zamantakewar ‘Yan Nijeriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: