Connect with us

RIGAR 'YANCI

NLC Na Son A Tsige Shugabannin Tsaron Kasa Muddin Matsaloli Sun Dore

Published

on

Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasar Nijeriya, Kwamared Ayuba Wabba, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tashi tsaye gami da gaggauta shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan, yana mai cewa Nijeriya ba ta cikin aminci na zaman lafiya.

Shugaban Kwadagon ya shaida hakan ne a wani taron manema labaru da suka kira a Abuja jiya Talata, yana mai cewa, akwai bukatar a yi mai iyuwa domin kawo karshen matsalolin tsaro.

Wabba wanda yake magana a madadin kungiyar Kwadago, ya kara da cewa, a kowani lokaci mayakan Boko Haram suna kara cin karensu babu babbaka wanda hakan na kara janyo abin mamaki ta yadda suke kara ci gaba da aikata miyagun aiyukansu.

Da aka tambayeshi dangane da ra’ayinsa kan tsige shugabanin tsaro ko barinsu a kan kujerarsu, sai ya kada baki ya ce, “Bana son shiga siyasar su tafi ko su ci gaba da jan ragamar hidimar tsaro.

“Abun da muke bukata kawai shine matsalolin nan a shawo kansu. Idan matsalolin tsaro suka ci gaba da faruwa to lallai ya dace su tafi, wannan shine matsayar da shugaban kasa Muhammad Buhari babban Kwamandan Askarawan Nijeriya ya dace ya dauka. Amma muna son inganci, aminci; muna son a shawo kan matsalolin tsaro, fatanmu matsalar tsaro ya kawo karshe,” A cewar Wabba.

Dangane da yunkurin baya-bayan nan da hukumar (RMAFC) na neman sake waiwaye kan albashin masu rike da mukaman siyasa a fadin kasar nan, kungiyar gwado ta kasa (NLC) ta yi kira da babban murya na a sake yin nazari da waiwaye kan albashin dukkanin jami’an da abun ya shafa.

Shugaban kungiyar ta kasa, Kwamared Ayuba Wabba ya kara da cewa, masu rike da mukaman siyasa a kasar nan ana biyansu kudade fiye da kima, “Albashin masu rike da mukaman siyasa a kasarmu ta Nijeriya ya zarce na kowace kasa a fadin duniya,”

A cewarsa, da ma’aikata da masu rike da mukaman siyasa suna gwagwarmaya daya da bukatun rayuwa iri guda, “Muna zuwa kasuwa don yin cefane iri guda ne da su,”

“A tunani na, ya kamata ne a ce albashin ma’aikata ne kan gaba fiye da na masu rike da mukaman siyasa,” A cewar shi.

Wabba ya kara da cewa, a wasu sassa kamar kasar Afirka ta Kudu akwai banbanci tsakanin kason ma’aikata da masu rike da mukaman siyasa.

Wabba ya nuna takaicinsa kan cewar a daidai lokacin da ma’aikata ke amsar albashi mafi karanci a kan kudi naira dubu 18, ita kuma hukumar RMAFC tana kan waiwayen albashinta zuwa kashi 800.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: