Connect with us

TATTAUNAWA

Rayuwar Sarkin Zazzau Makaranta Ce Babba Ga Shugabanni – Galadiman Zazzau

Published

on

Ranar 8 ga Fabrairun, 1975, rana ce da tsohon gwamnan mulkin soja na tsohuwar jihar Kaduna, Kanar Abba Kyari, ya tabbatar da nadin Alhaji Shehu Idris a matsayin Sarkin Zazzau. A wannan shekara ta 2020, Mai Martaba Sarkin Zazzau ya cika shekara 45 kenan a karagar mulki.

Wakilin LEADERSHIP A YAU, ISA ABDULLAHI GIDAN BAKKO, ya sami zantawa da daya daga cikin babban dan majalisar Mai martaba Sarkin Zazzau, wato GALADIMAN ZAZZAU, ALHAJI NUHU ALIYU MAGAJI, inda ya amsa tambayoyin wakilinmu kan yadda sarkin ya ke gudanar da mulki da yadda halayensa suke da kuma babban burinsa a rayuwa.

Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

 

Mai girma Galadiman Zazzau, a matsayin ka na wanda ya san mai martaba tun kafin ya zama sarkin Zazzau, ga shi kuma ka na cikin manyan ‘yan majalisar sarkin da suke ba shi shawarwari ga dukkanin al’amurra, ya ka dubi wadannan shekaru 45 da ya yi a karagar Zazzau?

Wadannan shekaru 45 da mai martaba sarkin Zazzau ya yi a matsayin sarkin Zazzau, abin alfahari ne da farko ga al’ummar masarautar Zazzau da jihar Kaduna da arewka da kuma Nijeriya baki daya, kuma abin godiya ne ga Allah day a zurtamu da wannan bawan Allah, da a duk rana, tunanin al’umma shi ne a zuciyarsa.

 

A matsayin ka na daya daga cikin makusantarsa dare da rana, tun kafin ma ya zama sarkin Zazzau, me za ka ce kan halayensa kan nauyin da mai kowa mai komi ya dora ma sa shekara 45 da suka gabata?

To, ka yi babban tambaya, domin a cikin dan kankanin lokaci, mutum komi kusantarsa da mai martaba sarkin Zazzau, zai wuya ya bayyana ma ka halayensa, sai dai in ce maka rayuwarsa kafatan, makaranta ce da mu ke koyon darussa da ba su misiltuwa, domin a duk rana da mu ka zauna da mai martaba ak majalisa domin tattauna wasu lamurra, ba ma tashi wannan zama da shi, sai mun sami darasin rayuwa ta shugabancin da dukkanmu ba mu sani ba. Ammma a takaice, kadan daga cikin halayem mai martaba sarkin Zazzau, su ne hakuri da hangennesa da kau da kai da furuci mai taushi da kyauta da ibada da tausayi da rashin mantuwa da neman shawarwari da karban shawarwari da kuma sauraron dukkanin wadanda suke zuwa wajensa kan wasu matsalolinsu ko kuma na al’ummarsu.

To ka ga, in an ce abubuwan nan da na bayyana ma ka, zan yi ma ka bayaninsu dalla – dalla, sa’o’I nawa za mu yi kan wannan tattaunawa kan wannan bawan Allah? Shi ya sa na ce ma ka rayuwarsa, makaranta ce, da in ko da rana guda ka sami zama da shi, ko kuma sauraronsa, za ka sami wasu darussan rayuwa da za su zama ma ka matakin da za ka inganta rayuwar ka ko kuma na al’ummar ka. Amma muhimmai a cikin wadanda na bayyana ma ka su ne, shi mutum ne mai hakuri, ban taba ganin fushinsa ba, mai tattalin zaman lafiya, duk jawbinsa, sai ya yi Magana kan mu bayar da gudunmuwa kan zaman lafiya, mai tallafa wa ne kan ilimi da sana’a ga al’umma, ban san yawan ‘ya’yan al’umma da ya dauki nauyin karatunsu ba, mai girmama gidajen sarauta na Zazzau, babu gidan da runguma da hannu biyu ba, mai tunanin zaman lafiya ne, duk wata matsala ta rashin zaman lafiya, ya kan tuntubi gwamnan ko wace jiha a Nijeriya, ya na tuntubar shugaban kasa kan ko wace irin matsala, ya bayar shawarwari, kuma an sami mafita da yawa daga shawarwarin da ya ke bayarwa,to, ka ji kadan daga cikin kyawawan halayen mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

 

Ya za ka kwatanta mai martaba sarki da sauran shugabanni bisa nauyin da Allah ya dora ma su?

A gaskiya a rayuwa ta, tun kafin mai martaba sarki ya zama sarkin Zazzau har zuwa yau ina tare da shi, ban taba ganin shugaba mai saukin kai ba, mai karban shawara mai rungumar kowa da kowa da kuma rashin mantuwa, domin zai iya ba ka labarin wasu abubuwa na fiye da shekara saba’in, kuma duk abin da mu ka tattauna a majalisa a yau, gobe in za mu ci gaba, ba sai an yi ma sa tunin inda aka tsaya a jiya ba, ka ga in ka duba shekarunsa fiye da tamanin, in ya yi mantuwa, ba abin mamaki  ba ne?

 

Mai girma Galadiman Zazzau, in na fahimce ka, mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, ya tanadi abubuwanda za a dade ana tunawa da shi ke nan?

Wannan tambaya da ka yi haka ne, a duk rana ya na barin darussan rayuwa, na kiran a zauna da juna lafiya, a girmama ra’ayoyin juna, na hakuri da ko wace matsala da ta shafe shi, na kula da matsalar da ta shafi al’umma, ga kuma darussan rayuwa da a duk rana ya na furta su da bakinsa da ayyukansa da kuma umurninsa.Wadannan abubuwa, suna cikin kadan daga cikin abubuwanda za a ci gaba da tunawa da mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris a shekaru da dama  ma su zuwa, domin shi babban burinsa su ne, shugabanci nagari da tallafa wa al’umma da tattalin zaman lafiya da talla wa marasa karfi da kuma tallafa wa addinin Musulunci, a kullun Amu ma wadannan abubuwa mu ke yi, domin koyi da shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: