Connect with us

SHARHI

Yadda Manyan Jaridun Kudu Suka Binne Labarin Dan Kunar Bakin Waken Kaduna

Published

on

Wani abu da ke kara cigaba da daure wa al’ummar Nijeriya kai, musamman Musulmai shi ne, yadda wasu manyan jaridun da ke kasar, musamman wadanda ke da shalkwatarsu a Kudu, su ka ki wallafa harin bam da a ka dakile a ranar Lahadin da ta gabata, wanda wani matashin Kirista mai suna Nathaniel Samuel ya so ya yi a cocin Libing Faith Church da ke yankin Sabon Tasha a cikin karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna.

Hakan ya ja hankalin ne ganin yadda duk da lamarin ya yi kamari a lokacin da a ka bankado kai harin na Nathaniel Samuel, mafi yawancin manyan jaridun kasar a washe garin Litinin 3, ga Fabirairu, 2020 yawanci a manyan rahotannin da su ka buga ba su dauki kai harin na Nathaniel Samuel ba.

Idan a ka yi la’akari da yadda Nijeriya ke cigaba da fuskantar na’ukan kalubalen ta’addanci, abin bakin ciki ne a samu irin wadanan manyan jaridun da nuna bangaranci da addini a yayin gudanar da aikin jarida.

Hudu daga cikin manyan jaridun bakwai da su ka yi burus da buga labarin a gaban jaridarsu ko kuma su ka binne labarin a cikin wasu labaransu sun hada da jaridun The Nation, Banguard, ThisDay, Daily Sun, The Punch da kuma The Guardian.

A daya bangaren kuma, kai ka ce kamar abin wani shiri ne, koda ya ke mun bar wa Allah sani.

Alal misali a ranar da Shugaban Kungiyar Kiristodi ta CAN na kasa ya gudanar da zanga-zangar lumana tare da magoya bayansa kan ikirarin da ya yi na ‘’yan Boko Haram na kashe Kiristoci a Nijeriya da kuma kan yadda yanayin da tsaro ya ke a kasar, inda yawancin manyan jaridun, kamar The Punch, Guardian, The Nation, Banguard, Daily Sun, duk sun wallafa hotunan shugaban na CAN, Fasto Adeboye, da sauran mukarrabansa a gaban fuskar jaridin nasu, amma su a ganin wadanan Jaridun, labarin na Nathaniel Samuel ba shi da wani muhimmanci a kansa.

Masu karatu da dama, sun yi mamaki kan irin wadanan kanun labaran na wadannan jaridun da a ka ambata a sama.

Amma shin idan da dan kunar bakin waken Nathaniel Samuel ya ci nasara a ta’addancin da ya so ya aikata, da labarin ya zama wani abu na daban, musamman ganin cewar, za a yi ta danganta kai harin ga wadanda ba su ji, ba su kuma gani ba.

A ganina, hakan ya nuna a zahiri, wadannan jaridun su na sane da wani tuggun da a ka kulla, don a cimma wata manufa, sai kuma ikon Allah ya tona asirin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: