Connect with us

LABARAI

Daliban Jami’a Sun Bada Gudumawar Jini A Nasarawa

Published

on

Daliban Jami’an Gwamnatin tarayya da ke garin Lafia a jihar Nasarawa, sun ba da gudumawar Jini ga Asibitin Dalhatu Araf da ke Lafia.

Gudumawar Jinin ya biyo bayan gangamin wayar da kai da Malaman kiwon lafiya da ke Asibitin Dalhatu Araf su ka yi wa daliban a harabar Makarantar da ke Mararrabar Akunza.

Dalibai maza da mata sun yi ta tururuwa zuwa gurin da aka ware domin gwaji da kuma karbar jini a cikin Makarantar.

Da yake zantawa da Manema Labarai, Dakta Bello Sirajuddin, Babban jami’i a  sashen kula da jini na Asibitin Dalhatu Araf ya ce; suna gudanar da wannan gangamin ne na tsawon kwanaki biyu.

Ya ce; mun fara daga yau Laraba za mu gama a ranar Alhamis . ya ce; mun fadakar da mutane mahimmancin ba da jini. “Saboda sau da yawa rashin ba da jini yakan haifar da illa ga mutum.

Ya na da mahimmanci mutane su rika ba da gudumawar jini a kai a kai. Idan a ka dibi jini a jikin mutum ya na kara masa lafiya.”

Ya kara da cewa; bayar da jini yakan magance wasu cututtuka da ke jikin dan Adam. Kuma yana maganin hawan jini da sauransu.

Ya ce ; ” jinin nan da muke karba mu ma ceton rai za mu yi da shi, ba saidawa za mu yi ba. Sau da yawa a kan kawo marasa lafiya da suka yi hadari ana bukatar jini da gaggawa, idan ba a samu ba har jini ya kare a jikin mutum sai ya mutu.

Amma idan akwai irin wannan jinin a kasa sai mu yi masu amfani kuma su samu lafiya.

Wannan shi ne makasudin abin da ya sa mu ke karban wanan jinin a gurin jama’a “.

Ya yi kira ga dalibai da su rika zuwa a na gwada jinin su a kai a kai saboda za su iya fahimtar wani irin jini suke da shi. Kuma ya ya yawan jinin yake sannan babu cuta a cikin sa.

Ya ce; rashin binciken ya kan sanya cuta ya shiga jikin mutum amma ya kasa sani har sai ya haifar masa da matsala.

Wasu jama’an da suka bayar da gudumawar jinin sun yi godiya da shawarar da Malaman Asibitin suka ba su, suka kuma fahimtar da su mahimmancin ba da jinin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: