Connect with us

DAUSAYIN MUSULUNCI

Salatin Da Allah Yake Wa Annabi Muhammadu SAW

Published

on

Masu karatu, karatunmu na yau yana dauke da darasi ne cikin sanarwar Ubangiji Tabaraka wa Ta’ala ga halittu bayinsa da cewa shi kansa (Tabarka wa Ta’ala) yana wa Annabi Muhammadu (SAW) Salati. Kuma Mala’ikunsa su ma suna yi, sannan Muminai daga cikinmu su ma su rika yi.

Allah Tabaraka wa Ta’ala ya ce, “Lallai Allah da Mala’ikunsa suna Salati ga Annabi Salati, ya ku Muminai (wadanda suka yi imani) ku yi salati a gare shi, ku gaishe shi gaisarwa”. Allah ya nuna falalar Annabinsa da girmansa (SAW), tun da ya ce da kansa (SWT) yake wa Annabi Salati. Haka nan Allah ya nuna girma da falalar Annabi (SAW) tun da Mala’iku kaf dinsu suna masa Salati. Sannan Allah ya umurci bayinsa su yi wa Annabi Salati da gaisuwa.

Malam Abubakar Danforaki ya ruwaito sashen malamai sun fassara fadar Annabi (SAW) cewa “an sanya sanyin idona a cikin Sallah”, ba ana nufin Sallah ba ne a nan, Manzon Allah yana nufin an sanya sanyin idonsa ne a kan Salatin da Allah yake masa, da Salatin da Mala’iku suke masa da kuma horon da Allah ya yi al’umma ta yi ta masa Salati har zuwa ranar tashin kiyama, (wato Salatin da Allah yake wa Annabi Muhammadu SAW ai ya ishe shi jindadi).

Malamai sun yi bayanin cewa shi Salatin Annabi saboda girmansa har yau babu wanda ya iya yi, sai dai a mayar wa Allah Tabaraka wa Ta’ala a ce ya yi. Kuma saboda karamci na Allah Ta’ala, idan aka ce ya yi Salatin kuma ya yi, sai ya mayar da sakamakon abin ga wanda ya ce ya yi. Allah ake roka ya yi Salati ga Annabi Muhammadu (SAW), bayan ya yi sai ya bayar da sakamako ga wanda ya ce ya yi kuma ya ninka. Idan ba Salati ba, wace ibada ce take da wannan falala?

Wasu Malamai sun ce ma’anar Salatin Allah ga Annabi ita ce Rahama a gare shi (SAW). Ma’anar Salatin Mala’iku da na sauran Bayin Allah ga Annabi Muhammadu (SAW) kuma ita ce addu’a gare shi. Kila kuma aka ce Salatin da Mala’iku suke yi suna sa albarka ne da neman albarka. Amma mai Littafin (Ashafa) ya ce, a’a, Annabi ya bambance tsakanin Salati da Albarka (Manzon Allah ya ce ya Allah ka yi Salati ga Muhammadu kuma ka yi albarka ga Muhammadu SAW). Da albarka ita ce wannan Salatin; da ba a fadi Albarka daga baya ba. Sai dai in kuma Salatin ya kunshi Albarka bakidaya, sannan sai aka sake ambatar ta daga baya (kamar misali, wani ya ce ‘mutane sun zo daurin aurena har da wane’, ka ga ai ‘wane’ din nan shi ma mutum ne amma saboda wani abu ya sa aka kebance shi da ambato. Malam Alkadiy Iyad ya ce Manzon Allah ya bambance lafazin Salati da na Albarka yayin da yake fadar Salati a gare shi.

A cikin fassarar ayar nan ta farko ta Suratu Maryama (Kaaf, Hee… zuwa karshe), wasu Malamai masu ilimin magana sun ce wannan “Kaulasan” din ta farko tana nufin “tsarewar Allah, isuwar Allah ga Annabinsa (SAW)”. Allah Ta’ala a cikin Alkur’ani ya ce, “Shin Allah ba mai kiyaye Bawansa ba ne (Annabi SAW)?, ko har da ma wanda ya bi shi SWT). Ita kuma “Hababba” tana nufin “Shiriyar Allah Ta’ala ga Annabinsa”. Allah Ta’ala ya ce, “Kuma domin ya shigar da kai tafarki madaidaici”. Ita kuma “Ya’un” tana nufin “Karfafawar Allah ga Annabinsa”. Allah Tabaraka wa Ta’ala ya ce, “Allah shi ya karfafe ka da taimakonsa”. Ita kuwa “Ainun” tana nufin “Kiyayewar Allah ga Annabi (SAW)”. Allah Ta’ala ya ce, “Allah mai kiyayeka ne daga dukkan mutane (har da Aljannun ma gabakidaya)”. Ita kuma “Sadi” da ke ayar tana nufin “Salatin Allah ne ga Manzon Allah (SAW)”. Allah Ta’ala ya ce, “Allah da Mala’ikunsa suna Salati ga Annabi (SAW). Ya ku Muminai ku ma ku yi Salati a gare shi da gaisuwa”. Kenan duk abubuwan da wannan aya ta kunsa suna nuna girman darajojin Annabi (SAW) ne.

A wata ayar kuma, sakamakon wata rigima ta cikin gidan Annabi a tsakanin miji da mata da za a iya cewa babu hannun wani a ciki, amma har ita ma Allah bai yarda ba sai da ya shigar wa Annabi (SAW). Akan ce ‘tsakanin miji da mata sai Allah’, wannan magana haka take. Misali, tsakanin Sayyidina Zaidu da Sayyida Zainabu zaman aure ya ki dadi, da ya zo ya fada wa Manzon Allah, sai Manzon Allah ya ba shi hakuri ya ce masa ka ji tsoron Allah ka rike matarka (ka ga bai shiga tsakaninsu ba sai ya yi masa nasiha), amma da abu ya tsananta sai ya sake ta, ya zo ya fada wa Manzon Allah (SAW). Manzon Allah ya ce to Allah ya bai wa kowa alkhairinsa a cikinku. Don haka ba a shiga rigima tsakanin mata da miji, amma kuma ban da a janibin Annabi (SAW), Allah shigar masa yake yi.

Allah Ta’ala ya ce wa Sayyida Aisha da Sayyida Hafsatu (Allah ya yarda da su da iyayensu), “in kuka ga game wa Annabi kai ku biyun nan, (a fada muku) Allah zai hada kai da shi (Annabi SAW), haka Jibirilu (shi ma zai hada kai da Annabi SAW) da managartan Muminai, da duk Malaka’iku ma (za su hada kai da Annabi SAW”. An ce Sayyidima Umar (RA) ya karanta wannan ayar sai ya ce, “Subhanallahi, su waye wadannan mutanen guda biyu?”, sai Sayyidina Abbas (RA) ya ce, “da ‘yarka ce da ‘yar Abubakar” (RA).

Malamai suka ce, a cikin wannan aya an gane girma guda biyu; da girman Manzon Allah (SAW) da na Matansa. Ta bangaren girman Manzon Allah, wadannan matansa ne guda biyu da yake zaman aure da su cikin jindadi da wasanni na mata da miji, amma da suka taba shi dubi yadda Allah ya shiga masa rigimar, to matansa kenan na gida, ina ga kuma a ce wani kato ne daga waje, ina zai sha a wurin Allah in ya taba Annabi? Kuma an gane girman matan Manzon Allah (SAW), ‘yan mata ma a cikinsu. Sayyida Aisha (RA) har Manzon Allah ya koma ga Allah ba ta cika shekara 20 da haihuwa ba. Amma Allah ya ce musu idan suka hade wa Annabi kai, Allah zai goyi bayansa. Jibirilu ma zai shiga fadar, duk wani Mumini ma zai shiga, haka nan da sauran Malaka’iku ma. A wani wurin (managartan bayi), Malamai sun ce ana nufin da duk Annabawa ma za su shiga masa (SAW), ko kuma da Baban Aisha Sayyidina Abubakar da Baban Hafsah Sayyidina Umar. Kila kuma aka ce da Sayyidina Aliyu (RA). Kila kuma aka ce Muminai da za su shigar wa Annabi (SAW) rigimar su ne duk wani Mumini har zuwa tashin kiyama, duk za su shiga a hade wa mata biyu kai. Mata biyu fa, ka ga ai wannan yana nuna girman Matan Manzon Allah (SAW) ne, tun da har Allah da sauran wadanda aka lissafa za su taru saboda su.

Sai dai fa kuma, ‘yan’uwa a sani, wannan ba wani abu ne da zai sa wani ya zagi matan Annabi (SAW) ba, zamansu da Annabi (SAW) a matsayin matansa kadai ya isa kowa ya ga girmansu.

Za mu ajiye a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa za a ji mu da wani darasin, cikin yardar Allah. Alhamdu lillah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: