Connect with us

LABARAI

kungiyar ‘Yan Ta’adda Da Ta Fi Boko Haram Na Nan Tafe – Sultan

Published

on

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, yay i gargadin cewa, akwai yiwuwar samun wata sabuwar kungiyar ta Boko Haram, a sabili da sama da marayu 50,000 da ake da su a nahiyar arwwacin kasar nan.
Da yake Magana a wajen wani taro kan tsaro a kaduna, ranar Alhamis, Basaraken ya kuma yi tir da kafa rundunar nan ta Operation Shege-Ka-Fasa, wanda wasu gamayyar kungiyyin nahiyar arewacin kasar nan suka yi a yankin na arewa, inda ya nemi dattawannna arewa da su ja masu kunni, ya kuma nemi da kar a bari matasa su karbe shugabanci daga dattawan na arewa.
Ya ce matukar ba a yi wani abu ba a kan wadannan marayun, za su iya zama mafiya hadari da ‘yan Boko Haram, matsawar gwamnonin na arewa ba su yi wani abu ba a kai.
Ya kuma zargi ‘yan Bokon Arewa da tabarbarewar al’amurran yankin na arewa.
Sarkin Musulmin ya ce, “Tilas ne gwamnoni su yi duba yiwuwar yin wani abu domin magance matsalar tsaro, domin a yanzun haka akwai sama da marayu 50,000. Wadanda za su iya zama mafi hadari da Boko Haram, matukar aka kyale su suka taso ba tare da cikakkiyar kulawa ba.
“An gabatar da shawarwari masu yawa ba tare da an aiwatar da su ba, in kuma aka ci gaba da rashin aiwatar da su za mu ci gaba da zama a cikin wahala ne.
“Ba mun kasa samun mafita ne a kan matsalolin da suke fuskantar arewa ba, abin da muka rasa shi ne zartas da shawarwarin.
“Akwai wani kwamitin da gwamnonin arewa suka taba kafawa a karkashin jagorancin Talban Minna (tsohon gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu), aka umurci kwamitin da ya kewaya arewa domin neman mafita a kan matsalolin da suke addaban arewa din. Sai kwamitin ya kira ni y ace yana son zai fara ne da ni, kafin ya kewaya ya ga sauran Sarakunan, sai na cewa shugaban kwamitin, kar ka damu, ni zan tara dukkanin Sarakunan na arewa a Kaduna, domin ka ji shawarar mu a waje guda.
“An kuma yi taron a nan gidan gwamantin na Jihar Kaduna, ina iya tunawa da abin da na ce a wajen taron cewa mune muka haifar wa da kanmu matsalolin mu a nan arewa, in kuma muna son magance matsalolin namu za mu iya magance su, ba sai wani ya zo daga wani wajen ba domin ya magance mana matsalolin mu. A karshe, wannannkwamitin ya kamala aikin sa, ya kuma mika rahoton sag a gwamnonin na arewa, amma me suka yi a kai?
“A matsayina na shugaban majalisar Sarakunan arewa, na san mun rubuta wasiku tashi biyu a kan matsayarmu zuwa ga kungiyar gwamnonin nan arewa da kuma a wajen taron su a nan Kaduna, Ni da kaina na je nag a Gbongon Jos, Etsu Nupe da wasu mutane biyu, muka ba su wannan takardar. Babangida Aliyu shi ne shugaba a wancan lokacin, suka yi mana godiya suka kuma ce za su yi aiki da abin da yake a cikin takardar, amma har ya zuwa yanzun shekarar 2020, ban sake jin komai ba da wani.”
Sarkin Musulmin ya zargi ‘yan bokon na arewa a kan yanda suka kyale matasan arewa suka kirkiro na su kungiyar tsaron wacce take da motoci kwara biyu ko uku kacal. Na ga abin ne a talabijin, manema labarai kuma sun dauki rahotannin su. yanzun dattawa sun kyale matasa su shige gaba kenan. Don haka ‘yan siyasa su ne matsalarmu, dattawa su ne matsalarmu. In dattawa ba su yi jagoranci ba, matanasan za su yi abin da suka ga dama ne kawai, ina tunanin kuma sun yi daidai. Ya zama dole ku gargadi wadannan matasan ta hanyar ba su jagoranci nagari. Yanzun matasan sun kafa na su kungiyar tsaron. Ban ma san ko me suke kiranta ba, Operation Shege ka FASA”. Ko tana nufin me kenan oho.”?
“Don haka, ina yin kira ga dattawan arewa da su gargade su. ka da ku bari matasa su kwace shugabanci daga gare ku. Wannan ne ya sanya wannan kungiyar take da mahimmanci. Tilas sai ka riski kowa, komai kankantar sa. don haka ina ganin ya kamata mu shawo ta baki daya.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: