Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim din Khalifa

Published

on

Suna: Khalifa.
Labari: Fauziyya D. Sulaiman.
Tsara labari: Fauziyya D. Sulaiman.
Kamfani: G-TOP Multimedia.
Shiryawa: Muhammad MIA
Bada Umarni: Ali Gumzak.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Adam A. Zango, Ahmad Ali Nuhu, Nuhu Abdullahi, Rabi’u Rikadawa, Fati Washa, A’isha Aliyu Tsamiya, Nasir Naba da sauransu.
Fim din Khalifa, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani shahararren likitan kwakwalwa mai suna Dr. Sadik (Adam A. Zango). Shi dai Sadik ya rasa iyayensa tun wasu lokuta da su ka wuce hakan ya sanya ya ke zaune tare da kanin mahaifinsa wato(Rabi’u Rikadawa). Sai dai ba shi da wani buri sai na ya hada Sadik aure da ‘yarsa, saboda ya na kwadayin dukiyar da Sadik ya gada da kuma wacca ya tara da kansa tunda ya na da aikinsa mai kyau a hannunsa.
Sai dai shi a nashi bangaren Sadik ya na da yarinyar da su ka yi alkawarin aure, wanda su ka dauki dogon lokaci su na soyayya da ita mai suna Ramlat (A’isha Aliyu). Shi dai Sadik mazaunin garin Adamawa ne, yayin da ita kuma Ramlat ta na zaune ne a Kano. Sun hadu da Sadik a Kano ne lokacin da ya taba kawowa abokiyar karatunsa ziyara a nan Kano din mai suna Dr Khadija (Fati Washa). Sadik da Ramlat sun dade su na soyayya kuma sun shku da juna sosai, har sun ajje alkawarin cewa idan ya dawo daga karo karatu to za a yi aurensu.
Labari dai ya chanja a lokacin da Sadik ya dawo daga karo karatunsa daga kasar waje. Ya na dawowa gida ne, ya yi sallama da kawunsa, ya kuma shaida masa cewa zai tafi Kano domin fara aiki sannan ya na sa ran yin aure ma a chan. Sai dai Sadik ya yi mugun gani a lokacin da ya iso Kano ya riski a na auren Ramlat. Sadik ya samu kansa cikin mummunan tashin hankali wanda hakan ya janyo masa hatsarin mota, wanda ya zama sanadin samun ciwon laka. Sai dai ya samu kulawa mai kyau sanadiyar shigowar Dr Khadija cikin lamarin bayan ta samu labarin halin da ya samu kansa a ciki.
Zaman jiyar da Sadik ya yi a asibitin Dr. Khadija ne ya sa ya hadu da wani yaro mai suna Khalifa wanda shi ma mara lafiya ne a wannan asibitin, da yake asibitin daman na yara ne zallah. Sadik ya yi sabo da Khalifa saboda shi kadai ne ke debe masa kewa, sai dai shi ma ya rasa ransa a asibitin. A karshe dai Dr Sadik ya samu lafiya, kuma ya auri Ramlat sakamakon rasuwar mijinta.
ABUBUWAN YABAWA
1. Fim din ya tsaru domin labarinsa bai karye ba tun daga farko har karshe.
2. Fim din ya samu aiki mai kyau.
3. Fim din ya nuna muhimmanci yin halacci ga wanda duk ya yi maka, kamar yadda Dr. Khadija ta yi wa Dr. Sadik.
4. Hotuna, sauti, kalaman cikin fim din sun fita sosai ba tare da matsala ba.
KURAKURAI
1. A fitowar farko an nuna Sadik ya yi hatsari a Kano har an kai shi asibiti, amma kuma a fitowa ta biyu kuma an hasko kawunsa a Adamawa ya na cewa Sadik ya ce zai tafi Kano gobe.
2. Sunan da a ka kira fim din da shi wato Khalifa, sai sa mai kallo ya yi zaton fim din zai fi karkata ne a kan Khalifa din, amma sai gashi gaba daya rawar da Khalifa din ya taka ba ta da wani yawa da kuma tasiri a cikin fim din.
3. Ya ya a ka yi Ramlat ta kawo mijinta asibitin Dr. Khadija bayan tasan asibitin yara ne?
kARkAREWA
Fim din Khalifa ya samu nasarori da yawa, kuma ya yi nasarar isar da sakonsa ga masu kallo. Kuma nasarorin ba shakka sun rinjayi kalubalen da a ka samu a ciki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: