Connect with us

NAZARI

Abba Kyari: Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa

Published

on

Dukkan wata nasara da kowanne shugaban kasa zai samu tana da alaka ne da irin jajircewar shugaban ma’aikatansa; shi shugaban ma’aikata shi ne wanda ke aiki ba dare ba rana wurin samar da mafita, tabbatar da shiga tsakani da sauransu kafin a kai gaban Shugaban Kasa. Da yawan shugabannin ma’aikata sukan kasance mashawarta kuma na hannun daman shugaban kasa.

Tun bayan da aka nada shi a matsayin shugaban ma’aikata ga shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015, Mallam Abba Kyari ya yi ayyukan da suka nuna yadda shugaban ma’aikata ya kamata ya kasance. A karkashin wannan gwamnatin, Abba Kyari ya kasance mai daidaita lamurra a lokuta mabambanta. Biyayyar da Abba Kyari ke yi wa Shugaban Kasa Buhari ba ta da ta biyu, wannan ne ma babban dalilin da ya sa makiyan gwamnatin nan ke matukar jin haushinsa.

Kyari wanda masanin shari’a ne, kuma shahararren ma’aikacin banki ya siffantu da gaskiya da adalci. Shi kadai ya tsaya a idon baragurbin ‘yan siyasan da suka nemi su dakile yaki da cin hanci da gwamnatin Buhari ke yi. An yi ta kulla mishi sharruka da kazafi don kawai ya hana marasa kishin kasa cimma munanan muradinsu akan Nijeriya.

Ko ba a fadi ba, sanin kowa ne cewa, gwmanatin Buhari ta fi mayar da hankalinta kan ganin an samu aminci a tsakanin ‘yan kasa, wannan kuwa ta hanyar irin ayyukan ci gaba da gwamnatin ke samarwa. Daga bayanan da aka tattara sun tabbatar da cewa, salo da dabarun Abba kyari ne ke daidaita wannan kuduri na gwamnati.

An yi ta kirkirrar karairayi don a bata sunan Abba Kyari. Babban burin masu aikata hakan shi ne son wawitar da tsananin biyayyar da Abba Kyarin ke nunawa shugaban kasa Buhari. Su masu yin hakan ana daukar nauyinsu ne don dai a ga an haifarwa da tsarin gwmanati cikas. Mutane ne masu mummunar dabi’a, wanda sam Nijeriya ba ita ce a gabansu ba. Kuma sun sani cewa, ba su da gurbi a duk wata nagartacciya tafiya irin wacce Kyari ke jagoranta.

Bisa lura da irin yadda ofisoshin shugaban ma’aikata ke gudanarwa a sassan duniya, muna iya cewa Abba Kyari na daga cikin sahun farko na nagartattun da ake da su. Dabi’u uku da suka taimaka wa Kyari wurin cimma nasarori a ayyukansa sun hada da gaskiya, da kuma sanya aminci a zukatan mutane.

Yana da wahalar gaske mutane su aminta da mutum, sannan kuma babu wani abu mai saurin gushewa kamar aminci. Ana aminta da mutum ne a lokacin da ya fadi zance kuma ya cika. Saboda wannan kuma ya sa ‘yan Nijeriya suka aminta da shugaban ma’aikata Abba Kyari. Mafi muhimmanci a nan shi ne yadda ake da tabbacin cewa akwai amana a tsakanin Shugaban Kasan da Abba Kyari. Wannan kowa ya sani a fadin Nijeriya.

Wani Karin abu da ya sa Abba Kyari ya zarce tsara akwai batun yin hukunci. Saboda yanke hukunci na daya daga cikin muhimman abubuwan da duk wani shugaban ma’aikata ke bukata. Ko ba komi aikin shugaban ma’aikata shi ne shiga tsakanin ma’aikata da shugaban kasa. Sau da yawa shugaban ma’aikata na bukatar ya yanke hukunci cikin gaggawa a kan wani lamurran.

Na uku, shi ne kamala. Saboda kamalar Abba Kyari ya sa yake ci gaba. Shi ya sa duk lokacin da ya yi magana a madadin shugaban kasa, za ka ga komi ya fita fes babu tangarda. Saboda shugaban ma’aikata Abba Kyari ya san shugaban kasa sosai, ta yadda ya san abin da ya ke so da wanda ba ya so.

Abba Kyari ne ya samar da tsarin isar da sako mai inaganci tsakanin Shugaban Kasa da ma’aikatansa. Shi ke daidaita lamurra kafin a gabatar da su a gaban shugaban kasa. Daga nan kuma sai ya bayar da shawarwari kan matakan da ya kamata a dauka.

Irin wannan aikin ne wasu marasa kishin kasan ke tsammanin za a bayar ga mutumin da bai san inda kansa ke ciwo ba. Haushinsu da Abba Kyari shi ne an zabo nagartaccen mutumin da ya san tuggun duniya da yadda a ke magance shi.

Masu sukar Abba Kyari ba wai bisa rashin sani su ke aikata hakan ba. Su na da boyayyiyar ajandar aikata hakan. Burinsu shi ne su bata Abba Kyari a yunkurinsu na haifar da cikas ga gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Abba Kyari ya na da ilimi. Ya kammala digirinsa na farko a fannin ilmin kimiyyar sanin halayyar jama’a ‘Sociology’ a jami’ar Warwick da ke Kasar Ingila a shekarar 1980. Haka kuma ya na da digiri a fannin shari’a wanda ya yi a jami’ar Cambridge dake Ingila, inda ya halarci makarantar horas da lauyoyi ta Nijeriya a shekarar 1983. A shekarar 1984 ya yi digirinsa na biyu a Jami’ar Cambridge.

 

  • Mallam Gidado Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa, ‘Presidential Support Committee’
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: