Connect with us

LABARAI

Karya Yarjejeniya; NPA Ta Soke Hayar Filin Da Ta Ba Kanfanin LADOL

Published

on

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta qasa, ‘Nigerian Ports Authority (NPA)’ ta dakatar da hayar filayen dake Tarkwa Bay, kusa da Light House Beach a Legas data ba kamfanin na mai suna ‘Lagos Deep Offshore Logistics Base (LADOL)’ saboda karya kaidojin yarjejeniyar kwangilar da aka shirya tun da farko.
Hukumar NPA ta bayyana cewa, yin haka na daga cikin kokarin yaki da cin hanci da rashawa da shugaban qasa Muhammadu Buhari yake yi da kuma fatan haka zai karfafa wa masu zuba jari na cikin gida da qasashen waje.
Bayanin ya nuna cewa, kamfanin ta LADOL, ta bayar da hayar fulayen ne mai fadin hekta 11.2426 daga cikin hakta da ta yi haya daga NPA akan kuxaxe masu yawa ba tare da ta tuntubi hukumar NPA ba.
Bayanin ya kuma nuna cewa, kamfanin ta karbi tsabar kudi har Dala Miliyan 45 (daidai da Naira Biliyan 16.2) daga kamfanin ‘Samsung Heavy Industries Nigeria Limited (SHIN)’ wadda aka ba hayar hekta 11.2426, a ciki kuma Dala 524,105 (Naira Miliyan 37.73) ne kawai aka ba hukumar NPA.
Takardar wadannan bayanan wadda jaridar THISDAY ta samu ya nuna cewa, yayin da hukumar NPA ta bayar da hayar filin ga kamfanin GRML akan Dala 104,821.95 na tsawon shekara 5 (hekta 11.2426), sai gashi kamfanin na GRML ya kuma ba wa kamfanin SHI filin a kan Dala Miliyan 9 na tsawon shekara 5, abin dake nuna cewa kamfanin ya karbi Dala Miliyan 45, wannan kuma karya yarjejeniya ne kai staye .
Jami’in watsa labarai kamfanin LADOL, Mista Kunle Kalejaiye, ya bayyana cewa, bashi da ikon yin magana kan lamarin saboda tuni suka miqa lkamarin a gaban kotu.
Alummar Nijeriya dai na yaba wa matakan shugaban hukumar NP Ana yaki da cin hancu da rashawa, don hakan yana dawo da mutumnci Nijeriya yana kuma yi wa Nijeriya tsimin makudan kudade.m
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: