Connect with us

NAZARI

Me Ya Hana Buhari Amsar Kiran Sarkin Ningi Na Sulhunta Ganduje Da Sanusi?

Published

on

A ranar Alhamis da ta gabata ne Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, ya bukaci Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi wa Allah ya sulhunta rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.

Kwatsam kwana guda da yin kiran, sai ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito ya bayyana cewar ba zai shiga cikin rigimar ba, inda ya bayyana dalilansa da cewar, komai na tafiya ne bisa kundin tsarin mulkin kasa don haka ba zai yi karan tsaye wa dokokin kasa ba.

Kodayake LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewar tun kafin bukatar na Sarkin Ningin, kungiyoyi da daidaikun jama’a sun yi ta yin sa’ayinsu na ganin an samu sulhunta Sarkin da gwamnan na Kano amma lamarin ya ki kawowa karshen.

Hatta Dattawan arewa da Dattawa a jihar Kano, mashahuran mutane da kungiyar gwamnoni sun sha yin kokarin shawo kan matsalar Sunusi da Ganduje amma lamarin ya faskara.

Dattawan arewan sun taba kafa kwamiti ne mai mutum 10 da ya kunshi Alhaji Adamu Fika da Janar Muhammadu Inuwa Wushishi da Farfesa Ibrahim Gambari da Dr Umaru Mutallab da Dakta Dalhatu Sarki Tafida da kuma Sheikh Shariff Ibrahim Saleh.

Sauran ‘yan kwamitin wanda tsohon shugaban Nijeriya, Abdussalami Abubakar ke jagoranta, su ne gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi wanda shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ne da kuma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

Kwamitin sulhun da kungiyar dattawan arewa ta kafa domin warware rikici tsakanin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Sanusi, an yi tsammanin za su iya kawo karshen fitinar wanda jama’a da daman gaske suka sanya fatarsu na kawo karshen fitinar amma har zuwa yanzu da sauran burbudi.

Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi sun kwashe tsawon lokaci suna tafka rigima, da har hakan ya kai ga raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar, da suka hada da sarautar Rano da Karaye da Bichi da Gaya, baya ga sarautar cikin kwaryar Kano ta Sarki Sanusi II.

 

Da wadanne dalilai Sarkin Ningi ya kira Buhari ya shiga cikin matsalar?

Wakikilinmu ya nakalto cewar shi dai Mai Martaba Sarkin Ningi mai daraja ta 1, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shigo cikin matsalar da ya ki ci ya ki cinyewa  tsakanin Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi da kuma gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da tunanin Buharin zai tsoma baki wurin shawo kan matsalar.

Danyaya ya bayyana cewar matsalolin da ke ci gaba da faruwa na kara taba shaksiyyar Masarautar Kano, wanda ya bayyana cewar masarautar ta jima da tarihi mai kyau, inda ya bayyana cewar dukkanin wani abu na kawo wa masarautar cikas abun kaito da neman dakile shi ne.

A bisa haka ne ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaggadauta shiga cikin lamarin domin ci gaba da mutunta sarautu da masu sarauta.

A cewar shi, ba wai suna musun ko Sarki yayi laifi ko bai yi bane, illa dai suna neman a kawo karshen zancen ta hanyar yayyafa wa matsalar ruwan sanyi, a cewar shi, matsalar za ta iya zarce kan Sarkin har ta shafi dukkanin Kano da Jama’an arewa.

“Abinda na ke son a lura shi ne mu Sarakuna muna da dajararmu, yanzu kamar ni din nan ka duba jihar Bauchi dukkanin gwamnonin da aka yi a kan idona aka yi su, kusan guda 20 hudu a ciki sun rasu sauran suna nan,”

“Mu na da hakkin mu fadi gaskiya ko a dauka ko a bar mana. Kano tana da tarihi sosai, a duk kasar Hausa Kano ita ce jigo.

“Idan wani yayi laifi, abin da aka sani a addinin Musulunci shine yafiya, kuma kowa mai laifi ne. amma mun sha gani ana yafewa. Meye sa gwamnatin jihar Kano da jama’an jihar Kano da majalisar dokokin jihar; meye sa idan Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi yayi laifi meye sa ba za a yafe masa ba?

“Mun sani mutane a bayyane da wasu a boye an yi kokarin sulhunta lamarin nan, amma har yau abin nan ya gagara, ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa. Saboda haka, lallai ya zama wajibi mu kai wannan matsalar ga ubanmu, uban kasa Dattijo Muhammadu Buhari, shi kadai zai iya kawo karshen wannan matsalar, ya kuma sha yin hakan tun ba yau ba.

“Kuma ni ina da imanin Buhari na mutunta sarauta, don haka na ke rokonsa, wannan mutuncin da yake yi wa sarauta, don Allah don Annabi ya shiga cikin matsalar nan ta Kano domin a shawo kan matsalar a sulhunta tsakanin sarki da gwamnan jihar ta Kano,” A cewar Sarkin Ningi.

Sarki Sanyaya ya kara da cewa, “Kano shekara sama da dubu suke da sarauta tun lokaci Habe har Fulani suka zo, a arewa din nan babu sarauta irin tasu, sai dai a daraja Sokoto, Borno, da Gwandu iyayen gidanmu ne a daraja, amma sarauta tsurarinta sai Kano. Idan aka yi wulakanci wa Sarautar Kano to kowa sai ya shafa wa kansa ruwa, a saboda haka ne nake tsokaci a nan nake cewa ita gwamnatin jihar Kano ta yi hakuri, jama’an jihar Kano su yi hakuri, Mai Martaba Sarki ya yi hakuri, a hadu tare a kyautata jihar Kano da masarautar Kano.

“Idan an lura ita wannan hukuncin ‘ya’yan sarautar Kano, jama’ar mutanen Kano baki daya, da mu Sarakunan Arewa ko sarakunan Nijeriya gaba daya wannan hukuncin zai mana illa. Kamata ya yi a takaita wannan hukuncin ga inda ya auku. Amma yanda aka wargaza wannan al’amarin muna fatan a dai yi tunani akai zuciya nesa. Kano dole idan an yi tafiya irin wannan to dole ne wasu al’amura su dan ruguje, su ja da baya, to kuwa ba abu ne wanda zai yi wa kowa dadi ba, gama daga mutanen Kano, mu sarakunan arewa da ma na Nijeriya da kuma ‘ya’yan sarautar Kano,”

To sai dai duk da hujjojin da Sarkin Ningin ya dogara da su, Buharin ce ba zai shiga cikin maganar ba, lamarin da ya zo ma wasu jama’an kasa cikin bazata.

 

Mene ne dalilin Buhari na kin tsoma baki?

Shugaba Buhari ya ce, ba zai yi karantsaye wa kundin tsarin mulki ba, inda ya bayyana cewar lamarin matsalar Kano har ya je gaban majalisar dokoki don haka dole ya ja baya cikin lamarin.

Amma wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta aike wa manema labarai ranar Juma’a, bayan shugaban ya gana da wata tawagar al’umar Kano da ‘yan jam’iyyar APC wacce Gwamna Ganduje ya jagoranta zuwa wurin Shugaban, ta bayyana dalilan da suka sanya Shugaba Buhari bai tsoma baki kan rikicin ba.

Mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce, “Na san aikina a matsayina na shugaban Nijeriya. Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya fayyace ayyukan gwamnan jihar Kano, don haka da zarar a ka ce batu ya na gaban majalisar dokokin jiha (kamar yadda ya ke a kan Kano) shugaban kasa ba shi da damar tsoma baki.

“Na sha rantsuwar yin biyayya ga kundin tsarin mulki, kuma ba zan sauya matsayina ba,” a cewar Buhari.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: