Connect with us

LABARAI

Zan Ladabtar Da Duk Basaraken Da Ya Bari Aka Yi Tashin Hankali – Gwamna Lalong

Published

on

Gwamnan jihar Filato, Rt. Honarabul, Simon Bako Lalong, ya furta cewa tun daga yanzun nan duk wani sarki da ya bari a ka tayar da fitina a yankinsa har a ka kai ga asarar rayuka da dukiya za a latabtar da shi. Gwamna Lalong ya bada wannan gargadin ne a lokacin bikin karin girmama ga sarakuna uku da ke cikin karamar hukumar Shendam wanda a ka gudanar a filin wasan kwallo na ‘Mini Stadium’ na garin Shendam Hedkwatar karamar hukumar a a karshen makon nan da ya gaba.

Gwamna Lallong a lokacin da ya ke tabbarwa sarakunan da mukaman karin girman da a ka yi masu ya hore su da su zama masu gaskiya da rikon amana da yin adalci wajen bai wa kowa hakkinsa da kuma rugumar kowa daga cikin mutanen da ke karkashinsu.

Ya ce, “hakkinku ne ku ilmantar da al’ummarku bisa bisa sanin dokoki da manufofin gwamnati maimakon raba kawunansu.”

Gwamnan wanda ya sake tuna ce su bisa mahimman rawar da za su taka kasancewar yansu fitinu da rigingimu sai kara yaduwa ya ke a sakanin al’umma, ya ce ya zama tilas gare su su kara kokari wajen kawo zaman lafiya a sakanin al’ummarsu, kuma su zama masu lura da yanayin zaman al’ummarsu don su sami damar kai rahoton duk mutumin da suka ga ya na aikata ba dai dai ba.

Sarakunan uku, da a ka kara masu girma kuwa su ne Mai girima Miskoom Dabit Isa, mai daraja na biu, sai mai girma Long Derteng Miskoom Thomas Yunkwap mai daraja ta Uku da Long Jakpoe Miskoom James Laankwap, mai daraje na Uku bida bi.

Tun a fari a jawabinsa maigirma Long Gamai na al’ummar Gamai Miskoom Martin Shaldas, a madadin majalisar Sarakunan na jihar Filato, ya yabawa Gwamnan bisa cika  alkawuran da ya dauka wa al’ummar jihar kuma ya bukashe shi da ya kara daga sauran masarautun gargajiya da ke cikin fadin jihar sai ya tabbatar masa da samun cikakken hadin kai da goyon bayan sarakunan gargajiya da fadin jihar.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: