Connect with us

SIYASA

2023: Wata Kungiya Ta Bukaci Gwamnan Bala Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

Published

on

Wata kungiya mai suna ‘Strategic Initiative For Good Governance’ ta fito ta yi kira da babban murya wa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir na ya fito takarar shugaban kasar Nijeriya a zaben 2023 da ke tafe.

A wani taron manema labaru da suka yi a Bauchi, Ko’odinetan kungiyar na kasa, Kwamared Muhammad Abubakar Jibo, ya shaida cewar lokaci bai yi wuri ba; na su fara tattauna wanda zai mulki Nijeriya a zaben da ke gaba lura da abin da ya bayyana halin da kasar ke ciki.

Tun da fari dai, kungiyar ta fara nuna damuwarta a bisa hauhuwar matsalolin tsaro, da suka hada da garkuwa da mutane, ‘yan bindiga dadi, da sauran matsalolin da suka kira na kuncin rayuwa da jama’a ke ciki, “Matsalolin rashin aiyukan yi, cin hanci da rashawa, take hakkin bil-adama da suke kara ninkuwa a wannan lokacin,” A fadin su.

Kungiyar ta ci gaba da cewa, Nijeriya tana tsananin bukatar a shawo kan muhimman matsalolin da suka yi wa kasar katutu, don haka ne ta shaida cewar tunin ta fara nemi hanyoyin da za a yi wajen magance matsalar ta hanyar zabin wanda ya dace a 2023.

A cewar Muhammad Jibo; “Lokaci bai yi wuri ba da ya dace a fara sharan fagen zaben 2023 domin kasarmu Nijeriya. Kungiyar nan ta yi nazarin gwamnati mai ci ta kasa shawo kan matsalolin da suke addabar kasar nan, bihasali ma, gwamnatin ta kasa cika alkawuran da ta dauka wa jama’a a lokacin yakin neman zaven 2019 daya daga cikin shine matsalar tsaro,”

Ko’odinetan kungiyar sai ya ce, sun gano wanda zai iya share wa ‘yan Nijeriya hawaye, “Bayan tuntuba da wannan kungiyar ta yi a ciki da waje, ta gano cewar akwai bukatar a samu hazikin jarumin da zai iya shawo kan matsalolin da kasar nan ke fuskanta, don haka ne muka ga dan takarar da ya dace shine gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir,”

“Mun kai ga daukar wannan matsayar ne bayan nazari da duba tarihinshi da nasarorin da ya iya cimmawa a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya Abuja na irin salo da tsari, iya ririta dukiya, jan kowa a jiki wajen tafiyar da mulki, da hada kan jama’a don haka ne muka zabo shi. Mun kirayi gwamnan Bauchi, Bala Muhammad na ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023 ne a bisa bisa cancantarsa,” A cewar kungiyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: