Connect with us

RIGAR 'YANCI

An Gudanar Da Addu’ar Uku Ta Surukin Karamar Ministan Abuja

Published

on

A ranar Lahadi ne a ka gudanar da addu’ar kwanaki uku ta Marigayi Alhaji Aliyu, wato uban mijin karamar ministan kula da babban birnin tarayya Abuja, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar Alhamis cdin da ta gabata.

An gudanar da addu’ar ne a babban masallacin Juma’a na garin Lokoja, babban birnin jihar Kogi, da misalin karfe 11 na safe.

Cikin wadanda su ka halarci addu’ar sun hada da ’yan majalisar dokoki na kasa da na jiha da sarakunan gargajiya da limaman masallatai daban-daban da ke garin Lokoja da malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na jihar Kogi da ’yan siyasa da kuma al’ummar Musulmi bakidaya.

Da ya ke jagorantar addu’ar, babban limamin birnin Lokoja, Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban, ya roki Allah (SWT) da ya gafartwa Marigayi Alhaji Aliyu zunubansa tare da saka ma sa da aljanna a bisa ga hidimar da ya yi wa addinin Musulunci a lokacin ya ke raye.

Sheikh Sha’aban, wanda ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki, ya ce, mutum ne wanda ya yi wa addinin Musulunci da kuma al’umma hidima, sannan ya roki Allah da ya biya shi cikin taskarsa.

Kazalika, ya kuma yi addu’ar Allah ya bai wa iyalai da ’yan uwan marigayin, musamman karamar ministan babban birnin tarayya Abuja, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu da maigidanta, Alhaji Tijjani Aliyu, hakurin jure wannan babban rashin da su ka yi.

Sauran malaman da su ka gudanar da addu’oi su ma sun roki Allah ya ji kan Marigayi Alhaji Aliyu tare da bai wa ’yan uwansa jimirin jure rashinsa. Tunda farko Kafin a gudanar da addu’oin, sai da al’ummar Musulmi su ka karanta Alkur’ani mai tsarki izifi 60 da Dala’ilul Khairati, don neman gafara ga Marigayi Alhaji Aliyu.

Shi dai Alhaji Aliyu ya rasu ne a ranar Alhamis din da ta gabata a asibitin kasa na Abuja bayan ya yi fama da rashin lafiya kuma an yi jana’izarsa a makabartar unguwar Kura da ke garin Lokoja, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: