Connect with us

LABARAI

An Karrama Shugabar NPA Hadiza Bala Usman

Published

on

Ranar Laraba ne wata kungiya mai fafutukar kare darajar mata ta duniya mai hedikwata a kasar Birtaniya (These Executive Minds” (TEXEM) UK) ta Karrama Shugabar Hukumar Tashar Jiragen Ruwa Nijeriya NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman da lambar yabo ta musamman.
Kungiyar ta Isa babban ofishin hukumar ne dake Marina Legas karkashin jagorancin shugabanta, Emmanuel Ekwe.
Cikin jawabin kungiyar na dalilin Karrama Hajiya Hadiza Bala Usman, ta bayyana cewa, ta samu gaggarumin nasara a fannin yaki da cin hanci da rashawa wanda hakan ya taimaka wajen yi wa Nijeriya tsimin Miliyoyin Daloli a zaman ta shugabar hukumar, a kan haka suka yi kira ga mata a Afrika su rungumi akidar gaskiya da rikon amana irin na Hadiza Bala Usman.
A nata jawabin, Shugabar NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman ta godewa kungiyar a bisa karrama ta da suka yi ta kuma yi alkawarin cigaba da aiki don bunkasar Nijeriya a duk inda ta samu kanta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: