Connect with us

Nahiyar Afirka

Ana Ta Ce-Ce-Ku-Ce Akan Na’urar Zabe A Ghana

Published

on

Wani kwamitin zabe a Ghana, ya ce na’urar zaben Biometric da aka samar tun shekaru tara da suka gabata ta tsufa, kuma ba ta yin aiki sosai, don haka lallai akwai bukatar a tanadi sabuwa. Sai dai kuma wannan bayanin ya sha bamban da korafin hadakar kungiyoyin jami’yyun siyasa dake adawa da buga sabuwar rajistar masu zabe.

Daraktan fasahar sadarwa na babbar jam’iyyar adawa ta NDC Kwame Grifit, ya ce ko da yake tun a shekarar 2011 aka samar da na’urar, kuma an ci moriyar ta sosai har yanzu ta na aiki.

Daraktan ya kuma ce yana da muhimmanci a yi la’akari da cewa sau 81 kawai aka yi amfani da na’urar, da kuma sauran wasu kayan aikin na kwamfuta, amma hakan ba ya nufin sun tsufa.

Da yake mayar da martani, Atik Muhammed mamban kwamitin zaben ya karyata ikirarin, ya na mai cewa na’urorin ba su tashi aiki ba.

Don haka, hukumar zabe mai zaman kanta ta ke ganin ya dace a buga sabuwar ragistar masu zabe da za a iya dogara a kanta.

A saboda haka kwamitin ke ganin matakin hukumar zaben ya yi daidai, kuma ya zo kan lokaci. Mr. Muhammed ya kuma karyata ikirarin cewa buga sabuwar rajista tamkar barnar kudi ne. Ya na mai goyon baya ga hukumar zaben, akan ta kammala buga rajistar zabe akan lokaci don zaben kasar na wannan shekarar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: