Connect with us

LABARAI

Auratayya Da Almajirci: Shugaban FCE Katsina Ya Yaba Wa Mariya Durumin Iya

Published

on

Shugaban Kwalejin Ilimin Makarantar FCE da ke Jihar Katsina, Dakta Aliyu Idris Funtuwa, Wakilin Malaman Katsina ya bayyana Hajiya Malama Mariya Inuwa Durumin Iya, a matsayin gwarzuwar da ta taka muhimmiyar rawar gani wajen kokari tare da yunkurin warware matsalar Auratayya da ta Almajiranci da ma sauran matsaloli da Malamar ta yi rubutu akansu da nufin kamo bakin zaren matsalar da ke damun al’ummarmu a yau.

Shugaban Kwalejin ta Katsina, ya bayyana haka ne a lokacin bikin kaddamar da littattafai uku na Hajiya Mariya Inuwa Durimin Iya, wanda aka gabatar a Unguwar Gwammaja da ke cikin Birnin Kano.

Har ila yau, Wakilin Malaman na Katsina, ya kara da cewa kowa dai ya san Auratayyarmu da kuma harkar Almajiranci na bukatar gyara ta hanyar ilimi. Don haka, wannan babban aikin nata na rubuta wadannan matsaloli, abu ne mai kyau kwarai da gaske. Saboda haka, wajibi ne mu gode mata tare da shawartar marubuta da su yi koyi da ita wajen rubuta irin wadannan littattafai masu matukar ma’ana. Daga nan ne, sai kuma ya sayi kwafi biyu na littafin akan kudi Naira Dubu 200 nan take.

Haka nan, ita ma a nata jawabin, Malama Mariya Inuwa Durimin Iya, ta bayyana cewa babban makasudin rubuta wannan littattafi shi ne, domin gyaran tarbiyyar al’ummarmu, musamman ganin yadda abubuwa suka tabarbare a halin yanzu, shi yasa ta dukufa wajen ganin ta rubuta wannan littafi don bayar da tata gudunmawar musamman ga al’ummarta ta Hausa Fulani, da ma sauran al’ummar Nijeriya da duniya baki-daya.

Sannan kuma, ta yaba wa daukacin manya-manyan bakin da suka halarci wannan taron bikin kaddamar da littafi nata da sauran al’ummar da suka bayar da gudunmawarsu ta kowane irin fanni. Kazalika, taron ya samu halartar manyan baki da suka hada da Dakta Bala Muhammad BUK, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, Farfesa Muhammad Sani, Farfesa Isa Muktar BUK, Sanata Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, sai kuma Hon. Sha’aban Sharada da sauran makamantansu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: