Connect with us

WASANNI

Ba Zan Yi Ritaya Daga Wasan Dambe Ba, Cewar Ebola

Published

on

Fitatcen dan wasan damben gargajiya Muhammad Abdurrazak Ebola ya ce bai yi shirin yin ritaya daga wasan dambe ba duk da rade radin da ake ya dawa cewa yana dan da daina wasan na dambe a bana.

Ebola wanda ke wakiltar bangaren Kuda wanda ke daure hannunsa na hagu ya ce kawo yanzu babu wani dan wasa da zai iya kare mutuncin Kudawa kamar yadda yake yi saboda haka dole sai an samu wanda zai rufa masa baya idan ya daina wasan.

Dan wasan daga jihar Kaduna ya ce kawo yanzu babu wani babban dan dambe da zai iya tare yaki da zarar ya tunkaro Kudawa sannan ya kara da cewar Shagonsa Taufik dogon Ebola da Dan Alin Bata isarka suna namijin kokari da sauran matasa, to amma wasu damben yafi karfinsu shi ya sa har yanzu yake yin wasan.

Akwai manyan ‘yan dambe a bangaren Guramada da suke da jiki da karfi kamar su Dogo Mai Takwasara da Garkuwan Cindo Dogon Kyallu da Habu na Dutsen Mari da dai sauransu haka ma a yankin Arewa kamar Ali Kanin Bello su Bahagon Shagon ‘Yan Sanda sai namijin gaske.

Ebola ne ya fara lashe mota a damben Kano da aka fara, haka kuma ya kai wasan daf da na karshe a wasannin Kaduna a shekarar nan sannan Ebola ya kara da Bahagon Shagon ‘Yan Sanda a Abuja inda wasan ya kai da takaddama, aka bai wa Bahago mota.

Sai dai sun sake haduwa a wasan karshe a damben Kaduna a Marabar Nyanya jihar Nasarawa, inda Ebola ya buge Bahagon Shagon ‘Yan Sanda, kawo yanzu kisa uku da uku ne tsakanin Ebola da Ali Kanin Bello, yayin da Ebola ya yi nasarar buge Mai Takwasara 3-1.

Shi kuwa sai Sarkin dambe Garkuwan Cindo da ya ci mota biyu a kan Ebola, amma bai yi kisa a wasan farko ba sai a haduwa ta biyu ne Garkuwan Cindo ya buge Ebola haka kuma Bahagon Mai Takwasara ya buge Ebola a bara a Abuja, koda yake Taufik ya daukarwa Ebola fansa inda ya buge Bahagon Mai Takwasara.

A wannan shekarar ta 2020 Abdurrazak Ebola ya ce zai dauki fansa a kan Sarkin dambe Garkuwan Cindo da Bahagon Mai Takwasara sannan ya kara da cewar zai kafa tarihin da bai yi shi a baya a harkar dambe ba zai kuma tsaya ya ci gaba da kare martabar Kudawa.

A harkar dambe Ebola ya samu alheri da dama ya na kasuwanci da sauran hanyoyin da yake samun daukar nauyin ‘yan uwa da abokan arzuka sai dai bai yi aure ba kawo yanzu duk da cewa a na ganin a wannan shekarar zaiyi auren.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: