Connect with us

RIGAR 'YANCI

BASOVCA Ta Zare Kashi 5 A Tallafin Da Saudiya Ta Bai Wa Marayun Bauchi

Published

on

Hukumar Kula Da Marayu da Marasa Galihu ta jihar Bauchi wato (BASOVCA) ta bayyana cewar za ta zare kashi biyar-biyar daga cikin dari na kudaden Tallafin da kowani maraya ya samu daga kungiyar IIRO ta kasar Saudiyya domin yin hidimar rabar da kudaden da shi.

Shugaban Hukumar marayu da marasa galihun Honorabul Hassana Arkila Tawus ita ce ta shaida hakan a lokacin da take ganawa da ‘yan jarida jimkadan bayan bude bikin fara rabar da kudaden tallafin da yawansu ya kai miliyan 180 da Marayun Jihar suka samu daga hannun kungiyar tallafi ta kasa da kasa wato International Islamic Relief Organisation (IIRO) ta kasar Saudiyya.

A bikin da ya gudana a dakon taro na gidan gwamnatin jihar Bauchi, Arkila ta shaida cewar cikin miliyan 180 da suka fara rabarwa a jiyan za su cire kashi biyar daga ciki domin yin dawainiyar raban da kudaden ga masu cin gajiyarshi.

Ta kuma bayyana cewar kananan hukumomi hudu da suka hada da Bauchi, Maraban Liman Katagum, Misau da ‘yan Katagum suke cin gajiyar tallafin ta kasar na Saudiyya wadanda aka zakulo su sama da shekaru goma da suka gabata domin amfana da tallafin.

Ta ce, tun zamanin mulkin Gamna Isa Yuguda aka baiwa marayu sama da dari hudu tallafin kudaden, sai dai an samu jinkirin samun kudaden da ya shafe shekaru da dama, inda ta ce bayan zuwansu kan gwamnati sun yi sa’ayi da kokarin tabbatar da kudaden sun fito daga hannun kungiyar da ta yi alkawarin bayar da shi.

A cewar shugaban Hukumar marayun, “Daga cikin yaran nan wasu za su samu dubu dari 500, wasu 600 wasu dubu 700; an kasafta rabiyar kashi-kashi ne, bisa abin da aka samu a yau, wasu za su samu dubu 500, wasu 300, wasu dubu 100 wasu ma dubu 50 za su samu hawa-hawa ne bisa ga tsarin da aka yi. Zuwa gaba za a karasa sauran, amma a yau za a rabar da sama da naira miliyan 180 daga cikin kason,” a cewar ta.

Dangane da cire kason ta amsa da cewa, “Tallace-tallacen da muke yi a gidan rediyo don neman marayun da zuwan ma’aikata din nan daga Saudiyya da dukkanin abubuwan da ake yi din nan da motocin da muke turawa wadanda mutane su zo su koma, kama wuraren kwana, tsaronsu da komai da komai a cikin kudin wannan ma’aikata ake cire don aiwatar da wadannan. Amma dukka wadanda ba su kai a ce an cire kashi 30 daga cikin kudin maraya ko an cire masa kashi 13 ba, don haka sai muka yi nazari muka ga cewar cire kashi biyar zai yi domin marayun nan an yi ne don su, su samu cin moriyarsa.

“Yara 489 ne suka cikin wannan shirin, amma yanzu mun iya samu yara marayu mutum sama da 270, muna kuma ci gaba da bincike domin gano sauran yaran, amma mun yi amfana da kafafen sadarwa na cikin gida wajen neman wadannan marayun da su ke cikin wannan shirin, amma mun gano sama da shekaru goma da daukar jerin sunayensu wasu sun mutum, wasu sun kaura zuwa wasu gagaruwan, za mu yi iya kokarin tantance wadanda mu ka samu sauran kuma kungiyar da ta bayar da tallafin za ta fadi yadda za a yi da su,” a cewar Alkila.

A wani binciken da wakilinmu yayi, ya gano cewar tallafin an nemo shi daga kungiyar IIRO tun a shekarar 2008 wanda kudin bai kai ga samu ba sai a wannan lokacin.

Tallafin dai kungiyar ta bai wa marayun ne domin taimaka mu su ta fuskacin cigaban iliminsu, inda wakilinmu na nakalto wannan zango shi ne na biyu na rabar da wani bari daga cikin kudaden, sai dai a rabiyar ta farko wasu kungiyoyi sun yi zargin bai dace a na cire wani kaso wajen rabar da kudaden ba lura da cewar hukumar marayun jihar na samun tallafi da a ke cire daga cikin albashin kowani ma’aikacin jihar domin talafiyar da harkokin ma’aikatar marayun, inda su ka ce ya dace ne a yi amfani da irin wannan kudaden wajen daukar nauyin rabiyar da kudaden ga masu cin gajiyarshi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: