Connect with us

MANYAN LABARAI

Da Dimi-diminsa: An Kai Sabbin Hare-hare A Jiddari Polo, Maiduguri

Published

on

Rahotanni daga babban birnin jihar Borno, Maiduguri, sun bayyana cewa wasu mahara wadanda ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari a unguwar Jiddari Polo da ke cikin babban birnin jihar.

Wannan sabon harin, ya zo kasa da awanni biyu, bayan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai a birnin Maiduguri, inda maharan suka farmaki unguwar a daidai lokacin sallar magariba.

LEADERSHIP A Yau ta tattauna da jama’a da dama a Maidugurin, daga ciki akwai Malam Shettima Umar wanda ya bayyana cewa, ”yanzu haka sai karar harbe-harben manyan bindigogi inda jama’a kowa sai ta kansa yake yi”.

”Gaskiya al’amari ne mai daure kai, ganin cewa harin yazo yan sa’o’i kadan da ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a nan birnin Maiduguri. Wannan wane irin abu ne haka, wane laifi muka yi ne haka da har bamu cancanta mu samu kwanciyar ran mu ba”.

Wasu bayanan kuma sun tabbatar da cewa kararar bindigogin tana dan lafawa, sannan kuma jami’an tsaro na ci gaba da kai dauki a unguwar.

Ku biyo mu don jin cikakken labari…..
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: