Connect with us

LABARAI

Gashash Ya Maka Rundunar Sojojin Nijeriya A Kotu

Published

on

A jiya Talata ce, Sardaunan Matasan Nijeriya kuma mazaunin jihar Kaduna Alhaji Mohammed Ibrahim Gashash ya maka Rundunar Sojin Nijeriya a gaban Babbar Kotun Tarayya dake da zamanta a jihar Kaduna.

Gashash ya kai karar ce a gaban Mai Shari’a Alkaliyar Babbar Kotun ta daya dake Kaduna Z. B Abubakar.

A  hirarsa da manema labarai jim kadan da fitowa daga Kotun Gashas ya ce,  Sojojin sun kama ni suka kuma tsareni ba tare da wata kwakwarar hujja ba kuma ba tare da sun gabatar dani a gaban Kotu ba.

Ya ci gaba da cewa, sun lama ni a ranar daya ga watan Janairun shekarar 2020 lokacin da suka zo gida na da misalin karfe hudu na dare sanan kumasuka ce zasu chaje gidana.

A cewar Gashas, na tambaye su sunzo da takardar da zasu kama ni suka ce a’a na kuma tambaye su ko sunzo da takardar da ta basu umarnin su chaje gidana suka ce a’a.

Gashas ya bayyana cewa, sojojin a jikin kakinsu sun sun cire sunayen su wanda wannan ba daidai bane, inda ya kara da cewa, nace masu ba zan fita daga gida na ba a cikin wannan daren sai dai su bari da rana ido na ganin ido.

Ya sanar da cewa, sun kuma kara dawo gidana bayan kwanuka goma suka kewaye gida na har na tsawon kwanuka shida.

Alhaji Mohammed Ibrahim Gashas ya bayyana cewa, zaman na Kotu na yau, an gabatar da karar ce a gaban babbar Kotun ta Tarayya dake zamanta a jihar Kaduna.

Shi kuwa lauyan mai kare wanda ya shigar da karar a gaban babbar Kotun ta Tarayya  Barista Sani Malam Garba ya ce,  yau an fara sauraron karar da wanda yake karewa Alhaji Mohammed Ibrahim Gashas ya shigar akan Rundunar Sojin kan tauye masa yancin sa kuma Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Fabirairun shekarar 2020.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: