Connect with us

LABARAI

Gidan Rediyon Bauchi Ya Bukaci Wadanda Suka Mamaye Filinsa Da Su Tashi

Published

on

Hukumar Gudanarwa ta Gidan Rediyon Bauchi (BRC) ta nuna matukar damuwarta dangane da mamaye mata filinta na tsohon tashar watsa shirye-shiryenta da ke kauyen Tirwun a cikin karamar hukumar Bauchi da wasu suka yi ba tare da izininta ba.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru dauke da sanya hannun Manajin Darakta na gidan rediyon, Alhaji Sirajo Ma’aji, wanda ya rabar wa ‘yan jarida jiya a Bauchi, gidan rediyon ta nuna damuwarta ne kan yadda wasu da bata bayyana sunansu ba ke ci gaba da shiga mata muhalli da yin gine-gine a ciki.

Sanarwar ta bayyana cewar hankulanta sun karkata ne dangane da wasu masu kutse da suka kutsa cikin filin kana suka kama ginewa ba tare da sanin hukumar gidan rediyon ba, don haka ne hukumar gidan rediyon ta shaida cewar ko kadan ba za ta lamunci hakan ba, lamarin da ma ta bayyana gargadinta kan masu shiga mata fili da su tattara su bar wurin muddin suna son kansu da lafiya.

A cewar shugaban gidan rediyon, “Abun kaito da kyama kuma abin takaici ne mutane su yi ikirarin mallakar wani abun da suna sane ba nasu ba ne,”

“A daidai lokacin da muke tabbatar da cewar har yanzu BRC ce ke da mallakin wannan muhallin; muna amfani da wannan damar wajen gargadin duk wanda ya kutsa cikin muhallin ya tabbatar ya rushe duk wani gidan da yayi ba tare da bata lokaci ba, sannan ya tattara ya bar wannan muhallin cikin hanzari,” A cewar sanarwar.

Hukumar ta kuma shaida cewar BRC ta tattauna da Sarkin Tirwun da hukumar kula da muhalli ta jihar hadi da sauran kungiyoyin da abin ya shafa dangane da kiyaye filin daga masu kutse da ‘yan mamaya.

Shugaban gidan rediyon Sirajo Ma’aji sai ya nemi hadin kan hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da yin mai iyuwa domin kiyaye masu filinsu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: