Connect with us

KASASHEN WAJE

Gwamnatin Mali Za Ta Shiga Tattaunawa Da ‘Yan Tawayen Arewaci

Published

on

Shugaban Kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya bayyana tintibar yan tawayen kasar da zummar tattaunawar da zata haifar da zaman lafiya bayan daukar dogon lokaci ana kashe mutane a sassan kasar.

Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Keita ya bayyana cewa ya nada tsohon shugaban kasar Dioncounda Traore domin tattaunawa da Yan bindigar domin kawo karshen asarar rayukar da ake tafkawa a kasar.

Kungiyoyi da dama sun dade suna kira ga gwamnatin Mali da shiga tattauna da Yan tawayen domin ganin sun aje makaman su da kuma rungumar zaman lafiya, cikin su harda kungiyar ICG.

A daya wajen a jiya ne rundunar sojin Mali ta fara tura dakarun ta a Kidal dake yankin arewacin kasar ta Mali domin karbar tafiyar da ikon wannan birni mai matukar muhimmanci da ya fice daga hannun mahukumtan kasar na tsawon lokaci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: