Connect with us

WASANNI

Ina Rayuwar Pele Babban Darasi Ce Ga Dan Adam, Cewar Dansa Edinho Lashe Kofuna A Barcelona – Asisat Oshoala

Published

on

Dan wasa Edinho, daya daga cikin ‘ya’yan gwarzon dan wasan nan na duniya Pele, ya bayyana cewa, tabbas halin da mahaifinsa ya ke ciki ya ishi duk wani dan kwallo a duniya ishara cewa rayuwa ba komai ba ce.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwarzon tsohon dan kwallon kafar na duniya da Brazil, Pele na dari-darin barin gida, saboda ba ya iya tafiya ba tare da an taimaka ma sa ba, wanda hakan ya ke nuna irin girman ciwon kugun da dan wasan ya ke fama da shi a yanzu, kamar yadda dansa ya bayyana.

A bara ne a ka kai Pele, zakaran kofin duniya karo uku da a ke cewar babu kamarsa a fagen kwallon kafa a duniya asibiti, asibiti sakamakon faduwa da ya yi ya na tafiya sai dai daga baya likitoci  sun samu nasarar shawo kan matsalar da yake fama da ita.

Pele mai shekara 79, yana da matsalar kugu da ke yi masa ciwo, wanda ke bukatar abin da zai dunga taimaka masa, bayan da ake yawo da shi a keken guragu idan zai shiga mutane wajen shekara daya kenan.

Pele ya ci kwallaye 1,281 a wasanni 1,363 da ya yi kakar wasa 21 yana buga wasa, har da kwallaye 77 da ya ci wa tawagar Brazil a wasanni 91 da ya buga mata, kamar yadda kididdiga ta nuna.

Pele na fama da rashin lafiya a shekarun baya, har da aiki da likitoci suka yi masa a shekara ta  2015 kuma karo biyu ya sake komawa asibiti tsakanin watanni shida a lokacin da jikin nasa ya sake yin zafi.

Daya daga cikin manyan ‘ya’yansa, Edinho, ya ce Pele sarki ne a fannin kwallon kafa, amma idan ka kalli halin da yake ciki, baya iya tafiya, baya samun sukuni kamar yadda yake so saboda haka wannan darasi ne babba da duk wani dan kwallo zai dauka.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: