Connect with us

WASANNI

Ina Son Lashe Kofuna A Barcelona – Asisat Oshoala

Published

on

’Yar wasan Nigeriya, Asisat Oshoala, ta ce, ta na kishirwar lashe kofuna a kungiyar mata ta Barcelona, bayan da ta ci kofi na farko a gasar kwallon kafar Spaniya a matsayinta na ‘yar wasan Barcelona

Oshoala, mai shekara 25, wadda kuma ita ce gwarzuwar ‘yar wasan Africa ta wannan shekarar ta ci kwallaye biyu a wasan da Barcelona ta casa Real Sociedad daci 10-1 a ranar Lahadin data gabata, kuma hakan ya sa kungiyar ta lashe gasar Super Cup a gasar mata a Salamanca.

Oshola ta shaidawa manema labarai cewar abin murna ne ta kara cin kofi, bayan Copa Catalunya da ta dauka a bara kuma tana fatan wannan shine somin tabi a kofunan da zata lashe a nan gaba  a rayurta.

”Abin da na sa a gaba shi ne saka kwazo da samun nasarori kuma babu abin da zai dauke hankali na akan wannan manufar tawa har sai naga ina samun abinda zuciya ta takeso kuma zan yi iya kokarina.” In ji Asisat

Ta ci gaba da cewa ”Kawo yanzu mun buga gasar rukuni-rukuni da ta kofin zakaru na Champions League da kuma gasar Spanish Cup a bana, akwai jan aiki a gaba kenan na ganin mun ci gaba da tafiya mu na samun nasara.”

Barcelona wadda kawo yanzu ba a doke ta ba tana mataki na daya a kan teburi, bayan da take fatan lashe kofin a karon farko tun bayan shekara biyar kuma ana ganin a wannan lokacin babu abinda zai takawa kungiyar birki wajen lashe kofin.

Haka kuma Barcelona za ta fafata da Atletico Madrid a wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League a watan gobe idan har ta samu nasara zata buga wasan karshe tsakanin kungiyoyin Lyon ko kuma Montpellier duka ‘yan kasar Faransa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: