Connect with us

WASANNI

Juventus Za Ta Yi Zawarcin Guardiola A Kaka Mai Zuwa

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta fara shirye shiryen tuntubar kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola, domin ya koma kungiyar.

Ya yinda ya rage saura watanni 18 kwantiragin mai koyarwa ya kare a zakarun na kasar Ingila, tuni aka fara rade radin cewa yana dab da barin kungiyar domin samun wata kungiyar daban musamman kasar Italiya.

Duk da cewa Guardiola yana yawan nanata cewa yana fatan ci gaba da zaman kungiyar ta Manchester City har zuwa kakar wasa ta gaba, amma halin da kungiyar take ciki a yanzu na rashin tabbas yasa an fara tunanin zai iya canja shawara.

Tuni dai aka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Juventus zata iya neman mai koyarwar idan har ta tabbatar da cewa zai bar Manchester City inda kuma ta shirya rabuwa da kociyan kungiyar na yanzu, Mauricio Sarri, wanda har yanzu baiyi kakar wasa daya ba a kungiyar.

Rashin nasarar da kungiyar ta Jubentus tayi a hannun kungiyar Berona a gasar Siriya a satin daya wuce yasa yanzu kungiyar ta koma mataki na biyu akan teburin gasar inda Inter Milan wadda ta doke AC Milan ta koma ta daya.

Sai dai duk da haka a na ganin Jubentus din ba zatayi saurin korar Sarri ba duk da cewa akwai shakku a kan ko zai iya gina kungiyar wadda take da ‘yan wasa manya-manya ciki har da Cristiano Ronaldo.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: