Connect with us

LABARAI

Kasar Sin Ta Aiko Wa Nijeriya Da Magungunan Cutar Coronavirus

Published

on

Hukumomin kasar Sin sun aiko wa da Nijeriya da hanyoyin kariya da magance kamuwa da cutar da ta samo asali daga kasar ta Sin, Coronabirus, wacce kuma a yanzun haka ta halaka sama da mutanan kasar ta Sin 908, ya zuwa ranar Litinin din da ta gabata.

Ofishin jakadancin kasar ta Sin da ke nann Nijeriya ya tabbatar da kawo magungunan na coronabirus wanda kasar ta Sin ta rarraba wa kasashen Duniya, wanda suka kunshi sakamakon bincike, bayanin cutar ya zuwa yanzun, hadarin da ke tattare da cutar, binciken da aka gudanar a kan cutar da kuma hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar.

A cewar sanarwar, Ofishin jakadancin kasar ta Sin ne ya aike da bayanan a kan cutar ta coronabirus, wanda ya amso daga hukumar lafiya ta kasar ta Sin, wanda ya ce ya amshi jimillan wadanda aka tabbatar da kamuwar su da cutar har guda 40,171, inda kuma aka sami nasarar yi wa mutane 3,281 magani ta hanyar raba su da cutar kwata-kwata har ma an sallame su daga Asibiti.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: