Connect with us

LABARAI

Kashi 87 Na Matalautan Nijeriya A Arewa Suke – Bankin Duniya

Published

on

Sashen Arewa na Nijeriya ne ya ke kunshe da kashi 87 na matalautan Nijeriya, kamar yadda wani sabon rahoton Bankin Duniya ya bayyana.

Rahoton mai taken ‘Advancing Social Protection In A Dynamic Nigeria’, wanda bankin na duniya ya sake shi a ranar 28 ga Janairu, 2020, ya yi nuni da cewa, matakan inganta rayuwa da gwamnatocin Nijeriya su ka rika aiwatarwa a baya sam ba su yi aiki ba wajen magance hauhawar talaucin, sannan kuma ga matsalar rigingimu da su ka addabi kasar ba.

Rahoton na Bankin Duniya ya kuma ce duk da cewa Nijeriya kasa ce wacce Allah Ya albarkace ta da albarkatu daban-daban, amma ta fi kowace kasa a duniyar nan yawan kekasassun matalauta.

Haka nan, rahoton ya yi nuni da cewa, yawancin matalautan na Nijeriya duk a yankunan arewacin kasar ne a ke samun su, musamman yankin Arewa maso Yamma na kasar, inda kusan rabin matalautan kasar ta Nijeriya su ke.

“Talauci a nahiyar ta arewacin na Nijeriya karuwa ya ke, musamman a sashen Arewa maso Yammacin kasar ta Nijeriya.

“Kusan rabin matalautan kasar duk a shiyyar ta Arewa maso Yammacin na Nijeriya ne su ke, inda yankin na arewacin kasar ya ke kumshe da akalla kashi 87 na jimillan matalautan kasar a sakamakon binciken rahoton na shekarar 2016.”

“Talauci a yankin kudancin kasar ya na bisa kashi 12 ne. Yankin kudu maso kudancin kasar ya na samun raguwar talauci matuka tun daga shekarar 2011 zuwa 2016.

“Rahoton ya kuma nuna talaucin ya fi yawa ne a yankunan karkara na kasar a shekarar 2016. Kimanin kashi 64 na dukkanin mataulatan kasar a yankunan karkara su ke.”

Rahoton ya kuma alakanta talaucin a araewacin kasar nan da rikicin Boko Haram, kamar yadda rahoton na Bankin Duniya ya nuna cewa, yawancin matasan da su ke shiga cikin kungiyar ta Boko Haram, duk marasa aikin yi ne, wanda hakan ya kan mayar da su kangararru.

Sannan rahoton kuma ya yi nuni da cewa, rikicin na Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, wanda a ke yi tun daga shekarar 2014, ya faru ne a sakamakon rashin cika alkawarin ’yan siyasa.

Rahoton ya kara da cewa, “Yawaitan Annoba da rigingimu ya daidaita ‘yan Nijeriya masu yawa, musamman a yankin na arewa maso gabashin kasar nan. Kamar yanda rahoton ya nuna, akwai sama da mutane milyan biyu da rikicin ya daidaita a Nijeriya, ya zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2018.

“A shekarar 2018 kadai, sama da ‘yan Nijeriya 600,000 ne suka daidaita a sakamakon yawaitan annoba, sannan sama da ‘yan Nijeriya 540,000 duk an daidaita su a sakamakon rikicin.

Rahoton kuma na bankin na Duniya ya bayyana cewa baya ga rikicin, canjin yanayi ya sanya an samu karin wadanda suka rasa muhallan su a yankin na arewa da kuma tsakiyar arewa na kasar.

A shekarar 2018, ambaliyar ruwa ya shafi sama da kashi 80 cikin 100 na kasar, wanda hakan ya samar da akalla sama da mutane 600,000 sababbi na wadanda su ka rasa muhallan nasu.

An kuma alakanta rashin kyakkyawan shugabanci, mahimman ayyukan raya kasa, rashin ingantaccen Ilimi sannan da kuma rashin abubuwan more rayuwa a matsayin wasu daga cikin dalilan yawaitan na talauci a kasar ta Nijeriya.

“Nijeriya ce take da mafiya yawan yaran da ba sa zuwa makarantar Firamare a duk tsakankanin kasashen Duniyar nan, inda akalla yara milyan Tara na kasar ba sa halartar makarantar.

Hakanan rahoton na Bankin Duniya ya fadi cewa, ‘yan Nijeriya milyan 71 sam ba su samun tsaftataccen ruwan sha, sa’ilin kuma da ‘Yan Nijeriya milyan 130 ba su rayuwa a yanayi na tsafta mai kyau.

Sai dai duk rahoton ya yi nu ni da cewa lamarin ya fi kazanta ne a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yammacin kasar, inda kashi 25 zuwa 28 ne kadai suke da abubuwan more rayuwa kamar na lantarki, tsaftataccen ruwan sha da wajen zama mai tsafta.

A tsakanin shekarar 2011 zuwa 2016, rahoton ya nuna jimillan ‘yan Nijeriyan da suke rayuwa a cikin kekasasshen talauci ya karu daga milyan 57 zuwa milyan 74.

Da yake tofa albarkacin bakin sa a kan wannan rahoton na Bankin Duniya, tsohon mataimakin shugaban kasar ta Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya alakanta matsalar ta yawaita talauci a arewa din ne da rashin Ilimi da yawaitan tashe-tashen hankula.

Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Abdukadir Balarabe Musa, ya alakanta matsalar ta yawaitan talauci a arewan ne da karancin Ilimi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: