Connect with us

KASASHEN WAJE

Kotun Faransa Ta Ci Tarar Teodorin Obiang

Published

on

Wata kotun daukaka kara a Faransa taci tarar dan shugaban kasar Equatorial Guinea Teodorin Obiang euro miliyan 30 da kuma masa daurin talala saboda samun sa da laifin almubazzaranci da dukiyar talakawan kasar, bayan ta kwace kadarorin da ya mallaka.

Tun a shekarar 2017 kotu ta samu Obiang da laifin rayuwar kasaita da dukiyar jamaa wajen sayen motocin kawa da gidajen kasaita.

Rashin gamsuwa da hukuncin karamar kotun ya sa Obiang ya daukaka kara, amma kotu tayi watsi da karar inda ta tabbatar da hukuncin.

Masu gabatar da kara sun ce dan shugaban ya halarta kudaden haramun da suka kai euro miliyan 150 a Faransa, bayan wani bene mai hawa 6 da ya mallaka tare da wani katafaren gida.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: