Connect with us

LABARAI

Ku Fifita Ilimi Fiye Da Kudi- Sakon Peter Obi Ga Dalibai

Published

on

Tsohon gwamnann Anambra, Peter Obi ya shawarci dalibai da su fitita neman ilimi fiye da kudi. Peter ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da gidauniyyar Ichakporoko foundation, wata kungiya da ba na gwamnati ba domin tunawa da Marigayi Michael Abonyi, wani dan siyasa dan garin Obollo Etiti dake karamar hukumar Udenu ta jihar Inugu.

A sanarwar da Ike Abonyi, daya daga cikin amintattun gidauniyyar ya fitar, ya bayyana cewa Peter Obi cikin jawabinsa a taron ya yiwa daruruwan dalibai wadanda suka fito daga makarantun Sakandare dake yankin jawabi.

Obi ya ce shi neman ilimi abu ne da ya kamata a dauke shi da muhimmanci, inda ya ce dukkanin wata kasa dole ne ta bai wa bangaren ilimi muhimmanci saboda sai da ilimi kasa ke ci gaba.

Har wala yau tsohon gwamnan ya shawarci daliban da su bai wa bangaren kimiyyar zamani muhimmanci wajen bunkasa kawukansu ta yadda za su bai wa al’ummarsu gudummawa. Ya nemi daliban da ka da su bautawa neman kudi fiye da ilimi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: