Connect with us

ADABI

Littafin ‘Sai Na Aure Shi’ Na Maryam Alhassan Dan’iya (27)

Published

on

Ji ka ke tararas kwalbar ta tarwatse a kasa. Lubna wani ihu ta saki, wanda su duka sai da suka tsorata. Ta je ta cakumi wuyan Audu ta na duka ta ko’ina. Ganin da gaske take ya sa Audu ya ture ta iya karfinshi, ya nufi kofar fita, yunkurowa ta yi ta kuma cakumo shi, ta jefar da shi tare da sa wa kofar key. Nan ta shiga jibgan Audu da Jummai, babu abunda kake ji sai karan ihu da manya-manyan ashar da ta ke sakar mu su.

Ganin in suka bar ta za ta kassara su ya sa su ma su ka fara kokarin ramawa amma Lubna ta fi karfinsu ta yi musu duka sosai, duk sun ji jiki domin kuwa Audu ko motsa hannu ya kasa don ya fi cin duka ga jikin tsufa.

Ganin in ta bar su haka ba ta huce ba ya sa ta dauko slender din Gas ta bude, gas ya fara fita a daidai lokacin Elma ta shigo gidan jin warin Gas ya sa ta nufi inda take ji, ganin Lubna ta yi da ashana tana kokarin kunnawa da gudu ta kwace  tare da fadin “Lubna mene haka, me kike shirin aikatawa?”

Lubna ture Elma ta yi ta na son kwace ashanan amma Elma ta tashi ta yi waje da sauri ta yar da ashanan. Nan fada ya dawo kan Elma inda ta cakumo ta, ta fara dukan ta nan Elma ta ji zafi ita ma ta fara ramawa.

Su ka wa juna jina-jina duk suka fashe kayan falon. Amma duk da haka Lubna ba tai sanyi ba, domin wani karfi take ji a jikinta, Elma ganin ba ta da niyan barin rigiman ya sa ta fita da gudu tare da barin gidan domin ba za ta iya wannan jidalin ba. Lubna ta bi ta domin kamo ta amma ta mata nisa.

Falon ta koma ta kurma ihu tare da fadin “Shi ke nan na rasa Adnan.” Sai kuma ta fashe da dariya “Kai Wallahi sai na aure shi.” Birgima ta dinga yi a kasa tana ihun “Sai na aure shi, Wallahi sai na aure shi.”

Jummai ta tashi dakyar ta yunkura inda Audu yake amma ko motsi baya yi, kaman gawa haka ya koma. Dan lekawa ta yi ta ga Lubna a kwance tana surfa ihu ita ma duk ta fita hayyacinta, komawa ta yi tana kuka, domin rasa inda za ta fita.

Lokaci daya da-na-sani ya shige ta. Tabbas duk wanda ya kauce hanya sai Allah ya jarabce shi ta yanda ba ya zato, son abun duniya ya ja mata irin wannan wulakanci yanzu da girmanta a ka kama ta aka jubga inda a gidan aure take wa zai mata irin wannan cin zarafin?

Tabbas har da hakkin iyaye ga shi yanzu ba sa raye balle ta nemi gafara. Audu dake kwance kaman gawa ya dan fara magana cikin rawan murya yana fadin “Ruwa! Ruwa!!” Jummai cikin tsanar shi tace “Ai sai ka je ka nemo, ba ka daku ba ne shi ne kake fadin ruwa.”

Jin an fadi duka ya sa ya tashi dakyar yana zazzare ido. Ganin inda ya ke ya sa ya tuna abunda ya faru, kuka ya saki tare da fadin “Jummai ina take?”

Jummai ta ce “Ban sani ba, sai ka je ka duba. Wallahi Audu ka cuce ni da wannan tsinanniyar shawaran naka.” Audu ya ce, “Don Allah Jummai ki bar maganan nan mu samu mu bar wannan gidan da ranmu domin wannan kafurar matar ba ta da imani dkn tsaf sai ta kashe mu.”

Adnan dake gaban Mum yana mata maganan yaushe za a tura gidansu Lubna, Mum ta ce “Sai na yi magana da dangin babanka in ji sanda za su,” ya ce, “Mum ina za su kuma?”

Mum wani kallo ta yi masa irin na ka mai da ni sa’arka ko? Adnan shiru ya yi yana tunani lokaci daya ya ji kaman an cire mai wani abu a jikinshi, tashi ya yi amma jiri ya debe shi ya fadi kasa sumamme.

Mum cikin tashin hankali ta nufe shi tana fadin “Adnan!!” amma shiru, fita ta yi waje ta kira security dinsa, ta ce su sa shi a mota sai asibiti.

Likitoci suka taru a kanshi amma babu alaman akwai abunda yake motsi a jikinshi. Iya tashin hankali Mum ta shiga ganin Dr Sun kwashe wajan awa uku amma shiru. Mum ta kira Kausar ta fada mata halin da Adnan yake ciki tace ta sanar ma matansa.

Zeenat tana ji ta fara kuka, hijab ta sa suka fita sai da suka fada wa Basmah ita ma tace za ta zo anjima kadan. Koda suka isa asibitin sun sami Mum ta zabga uban tagumi, da sauri su ka nufe ta Kausar tace “Mum ya jikin nashi?” Mum tace “Har yanzu Dr bai ce komai ba.” Nan suka zauna suna jira har Dr ya zo ya ce su same shi office.

Bayan Sun shiga Dr ya dan yi rubuce-rubuce sannan ya kalle su ya ce, “Hajiya har yanzu bai farfado ba, mun yi iya kokarin mu, amma har yanzu.” Mum ta ce, “Dr me ke damunshi?”  Dr yace “Gaskiya har yanzu ba mu gano ba amma mu na bincikawa.” Mum tace “Dr ko za ka rubuta mana takarda mu fita da shi waje?”

Sai ya amsa mata da cewa “Hajiya ku yi hakuri zuwa nan da kwana biyu, don gaskiya daga shi daga nan akwai matsala domin komai na jikinshi ba ya motsi yanda ya kamata, gara a bar shi.” Zeenat tunda Dr ya fara bayani take kuka cikin tashin hankali ji take kaman ta dauke mishi ciwon.

Adnan dai anata magani amma shiru kaman ba a yi, hankalin Mum ya kara tashi sosai. Kausar ta fada wa Hajiya abunda ya faru tun daga neman auren nashi har ciwonsa. Hajiya tace za ta tawo Abuja ita ma. Hakan ko a ka yi a ranan ta zo Abuja. Asibitin aka fara kai ta. Adnan dai kaman yanda ya ke tun ranan da aka kawo shi har yanzu, yayi haske tare da ramewa. Hajiya ta kalli ‘yarta tace “Anya wannan ciwon ba zamu gwada na gida ba?”

Mum ta ce, “Hajiya Dr yace daga shi daga nan akwai hatsari.” “To amma dai bari in gwada masa wani magani.” Nan Hajiya ta jiga ganyen magarya a wani kofi, ta fara shafa mai a jiki ta ko’ina. Hannunshi ne ya dan motsa kadan. Mum tace “Hajiya kin ga ya motsa Wallahi.” Hajiya ba ta ce mata komai ba har ta gama ta kuma jika wani ta sa masa a baki. Tare da zuba mai habba da zaitun da ta hada.

Wani irin ajiyan zuciya ya yi. Mum dadi ne ya cika ta, ita dai Hajiya cigaba ta yi da abunda take yi. Wani kwalba na ga ta dauko tana shafa mai abun ciki, tashi ya yi yana bubbude ido tare da kallon wadanda su ke dakin.

Idonshi ne ya sauka a kan Zeenat hannu ya bude mata alaman ta zo. Zeenat cikin sauri ta nufe shi rungume ta ya yi, lokaci daya kuma ya kuma faduwa ya kwanta. Hajiya tace “Alhamdulillah! Magani ya fara aiki, yanzu sai mu bari ya farka.”

Mum tace hjy “Meke damunshi toh?” Hajiya ta yi murmushi tare da fadin “Akwai sihiri a jikinshi amma komai zai zama tarihi.” Sannan ta tambaya da cewa “Ina dayan matar tasa?” Mum ta ce “Tunda ta zo shekaran jiya har yau ba ta kara zuwa ba.” Jin haka Hajiya ta numfasa tare da cewa, “Allah ya kyauta.”

Adnan ya yi wajan awa biyu kafin ya tashi, bakinshi dauke da salati, kallon dakin ya fara yi yana mamaki me ya same shi. Zeenat da Kausar da ke dakin suka fara murna, da sauri Kausar ta fita ta kira Mum, Mum ta ce ta je ta kira Dr. koda suka shiga Zeenat na kusa da shi, Adnan ya ce, “Hajiya yaushe kika zo?” tace “Ba dole in zo ba kar mijin ya mutu ban gan shi ba.”

Dariya ya yi yace “Ai ke za ki riga ni mutuwa dan sai na kai ki har kabarinki.” Hajiya tace “Ai sai ka kashe ni.” Duka su ka sa dariya, daidai lokacin Dr ya shigo ya fara duba Adnan. Nan Adnan ya ce shi yau zai tafi gida, ganin komai normal Dr ya ce babu damuwa nan ya sallame su, su ka nufi gidan Mum. Bayan ya yi wanka ya ci abinci nan ya ke tambayan Mum abunda ya faru da shi. Mum ba ta boye mai komai ba, nan ya fara hawaye tare da fada wa Mum shi Wallahi bai ma san wata yarinya da yake nema ba. Mum tace ikon Allah nan ya roki Mum gafara a kan ta yafe ma sa duk da bai san ya yi ba, ta ce ba komai.

Ranar farin ciki duk ya kama su sai wajan karfe takwas Mum ta ce ya dauki matarshi su tafi dare ya yi. Nan suka yi musu sallama suka nufi gida. Adnan yana son rokon Zeenat a kan abunda ya mata wanda bai san ya yi ba duk ya ga ta rame. Bayan Sun isa ya kalli gefen Basmah.

Zeenat ita ta yi ciki, don haka ya nufi sashin nata ganin kofar a dan bude ya sa ya tura ba kowa a falon, don haka ya haura sama nishi ya fara ji cikin sauri ya karasa tare da fadin ko Basmah ce ba ta da lafiya. Amma abinda ya gani ya sa shi kaduwa matuka.

 

Za mu cigaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: