Connect with us

LABARAI

Mun Jajirce Wajen Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Nijeriya- Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta jajirce wajen ganin ta kawo karshen matsalar rashin tsaro  da ta’addancin da ya addabi kasarnan.

Buhari ya bayyana hakan ne a garin Addis Ababa na kasar Habasha a jiya Talata a yayin wani zama da ya yi da ‘yan Nijeriya mazauna kasar Habasha da kuma shugabar hukumar dake lura da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.

A yayin da Buhari ke jawabi an yi shirun minti guda domin jajantawa ‘yan Nijeriya da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kashe a ranar Litinin a jihar Borno. Inda Buhari ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su bai wa hukumomin tsaro goyon baya wajen hadin kan kasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: