Connect with us

RAHOTANNI

Muna Samun Cigaba A Kasuwar Notastin – Barista Uzairu

Published

on

Shugan kasuwar ’yan notastin kasuwar sayar da waya salula a karamar hukumar Funtuawa ta jihar Katsina wadda ta ke da sunan Sarkin Maska Idris Sambo Idris Memoriyal GSM Funtuwa, Barista Uzairu Mohammed Funtuwa, ya bayyana cewar, kasuwar ta ’yan Notastin kasuwar sayar da waya salula tana kara samun cigaba a yankin na funtuwa da jihar Katsina bakidaya.

Barista Uzairu Mohammed Funtuwa ya yi wannan huruci ne a Funtuwa a ofishin kasuwar a lokacin da yake fadar albarkacin bakinsa agameda cigaban da yake ganin kasuwar tana kara samu a kowane lokaci kuma yake shaida ma jaridar Leadership a yau mai farin jini Jaridar hausa mai fitowa kullum jin dadinsa a gameda wannan alamari.

Ya cigaba dacewar, cigaban da kasuwar tasu ta yan notastin take kara samu sun hada da sama ma kasuwar lauya nata na musamman wanda zai tunkari duk kan wata matsala ta kasuwar idan hakan ta taso san nan kuma injishi suka samama kasuwar ofis dinta na dun dundun kuma suka budema dukkan dan kasuwar wanda yake cikin kungiyar kasuwar fayil tareda yimasu aidi kat domin tabbatar dasu cikakkun yan kasuwar ne bakidaya.

Sannan ya kara da cewar kuma suka Gyara ma kasuwar Fuska dagina ma yara makarantar isilamiya tareda bayuka wurin zagayawar yara domin biyan bukatar kansu idan hakan ta taso sannan suka sayama matasan kasuwar kwallon kafa domin sucigabada motsa jikkunansu injishi. Kuma suna tallafama mambobin kungiyar da kudade a lokacin da wani daya daga cikinsu yasamu hidimar suna kokuma aure ko rashin lafiya ko fan nin kasuwanci na saye da sayarwa sannan suka haramta ma yara kanana kawo wayar salula domin sayarwa a wan nan kasuwa tasu ta yan notastin. Acewarsa Babban mutumma idan yakawo wayar zai saida sai yazo da kwalin ta injishi idanma bakone saiya kawo wanda zai tsaya masa sannan su saya subashi kudin sa ya ce, ko ahakama ma sun kama barayin waya wadanda suka sato a wadansu unguwarni sama da hamsin ta da lilin hakan wadanda suka kawo wannan kasuwa domin sai dawa kuma kowanensu anbashi wayarshi bakidaya.

Sannan yacigaba da kiraga Gwamnatin jihar katsina a karkashin jagorancin harzikin Gwamnan R. T HON Aminu Bello Masari daya tallafama yan kasuwar da jari na kudade kamar yanda yake tallafama sauran kungiyoyin yan kasuwar jihar ta katsina domin Gwamnatin sa ta cigaba da samun kudin shiga sama da yanda take samu abaya. Yakara da cewar akalla kungiyar kasuwar tanada mambobi samada dubu biyu masu gudanar da kasuwanci a kasuwar bakidaya san nan yakara da cewar a madadin shi da sauran yan kasuwar na notastin dake funtuwa suna isar da sakon godiyarsu ga sarkin maskan katsina hakimin Funtuwa Idris Sambo Idris tare da sauran jamian tsaro na funtuwa a wajan kare lafiyaryan kasuwar da dukiyoyin su bakidaya ya ce kuma wannan kasuwar tana maraba kowa da kowa domin gudanar da kasuwanci a kasuwar bakidaya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: