Connect with us

WASANNI

Na Koma Inter Ne Domin Lashe Kofi – Lukaku

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, Rumelu Lukaku, dan kasar Belgium, ya bayyana cewa ya koma kungiyar ne a wannan kakar domin ganin ya lashe kofin gasar Siriya A a rayuwarsa.

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta hau kan teburin gasar Siriya A, bayan da ta doke abokiyar hamayyarta ta AC Milan daci 4-2 a wasan mako na 23 da suka fafata a karshen mako a kasar ta Italiya.

Kafin karshen makon Inter tana ta uku a teburin, amma nasarar da ta yi ya sa ta koma ta daya da maki iri daya da zakarar gasar wato Jubentus, amma da tazarar cin kwallaye a gasar bayan da aka doke Jubentus din a wasan karshen mako.

A wasan na hamayya da kungiyoyin biyu suka buga, AC Milan ce ta fara cin kwallaye biyu tun kafin hutun rabin lokaci kuma Ante Rebic ne ya fara cin kwallo daga baya Zlatan Ibrahimobic ya kara ta biyu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Inter Milan ta farke kwallaye biyu ta hannun Marcelo Brozobic da kuma Matias Becino sannan daga baya ne Stefan De Brij da kuma Romelu Lukaku suka ci wa Inter sauran kwallaye biyun.

Kawo yanzu kungiyar Inter Milan tana mataki na daya a kan teburi da maki 54 iri daya da na Jubentus, sai dai Inter Milan tana da rarar kwallaye 28, yayin da Jubentus keda guda 21, bayan wasannin mako 23.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: