Connect with us

LABARAI

PSC Ga Dattawan Arewa: Babu Dattako A Sukar Buhari

Published

on

Kwamitin tallafawa shugaban kasa ya nemi Kungiyar Dattawan Arewa da ya bi a sannu wurin yin maganganu kan halin da ake ciki a Nijeriya, inda kungiyar ta ce, sukar gwamnatin Buhari da dattawan suka yi sam babu dattako cikinsa.

Idan dai ba a manta ba a ranar Lahadin da ta gabata ne Kungiyar Dattawan Arewa karkashin shugabancin Farfesa Ango Abdullahi ta ayyana cewa ba kawai gazawa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi ba kan harkar tsaro, a’a ta gaza samo hanyoyin daidaita matsalar ta tsaro da ake tsaka da fama da ita.

Sai dai a wani martani wanda kwamitin tallafawa shugaban kasa (PSC) ya fitar, ta hannun Daraktan Sadarwa da tsare-tsarenta Mallam Gidado Ibrahim, kwamitin ya ce, ya yi takaicin irin matakin da kungiyar dattawan arewa ta dauka, wacce kamata ya yi ta hada hannu da shugaba buhari wurin tseratar da Nijeriya daga halin da take ciki. Sai kuma suka buge da wulakanta kokarin da gwamnatin ke yi.

Ibrahim ya ce: “Mun tsinci kanmu cikin alhini da takaici dangane da dirar mikiyar da Kungiyar Dattawan Arewa suka yi wa gwmanatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. A tsammaninmu, tunda har kungiyar dattawan tana cike ne da dattawa, ai da sais u hada karfi da karfe wurin taimakawa gwamnati a irin wannan yanayi da Nijeriya ta tsinci kanta. Sai dai, su dattawan nan sam babu dattako a tare da su.

“Bayan sun alakanta rashin tsaro da talauci, Kungiyar ta dattawan arewa sun zargi gwamnatin Buhari da rashin samar da hanyoyin dakile matsalar tsaron. Sai dai a nan, wadannan dattawa sun kwafsa, domin a gaban idonsu gwamnatin Buhari ta yi amfani da kudaden Abacha da aka kwato wurin tallafawa talakawa duk don a rage kangin talauci.

“Ko har sun manta cewa an kirkiri ‘TraderMoni’ ne domin a taimakawa matasa wadanda suka kammala makarantun gaba da sakandare? Oho, ya fi kama da cewa, so suke yi shugaban kasa Buhari ya bude baitul mali a yi ta wasoso kamar yadda gwmanatin PDP ta yi a baya. Kila idan aka yi haka ne za su yarda ana yaki da talauci.

“Kungiyar Dattawan Arewa ba ta fada mana mene ne hakikanin manufarta ba. Kafin a san hakikanin manufarsu, ya kamata ’yan Nijeriya su ci gaba da watsi da zantukansu, don babu makama ko kadan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: